Home / Labarai / Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Nada Ahmed Nuhu Bamalli Sarkin Zazzau

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Nada Ahmed Nuhu Bamalli Sarkin Zazzau

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Nada Ahmed Nuhu Bamalli Sarkin Zazzau
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Nasiru Ahmad El- Rufa’i, ta bada sanarwar nadin Jakada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.
Kamar yadda sanarwar da kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi Jafaru Ibrahim Sani ya fitar a garin Kaduna cewa bisa wannan matsayi na Gwamnati a yanzu Ahmed Nuhu Bamalli ya zama shi ne Sarki na 19 kenan a jerin sarakunan masarautar Zazzau, inda ya Gaji marigayi Alhaji Dokta Shehu Idris da ya rasu a ranar Lahafi, 20 ha watan Satumba 3020 a asibitin sojoji na na 44 da ke Kaduna bayan kwashe shekaru 45 a kan Sarautar Zazzau.
Alhaji Bamalli shi ne Sarki na farko a gidan Mallawa a a bayan shekaru 100 bayan da kakansa Sarki Dan sidi ya rasu a shekarar 1920.
Kafin rasuwarsa Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli ya rike mukamai da yawa daga ciki har da sarautar Magajin Garin Zazzau kuma ya zama jaladan kasar Nijeriya a Thailand da kuma hadi da tsare tsaren Myanmar.
Ya kuma zama kwamishinan dindindin a hukumar zabe ta Jihar Kaduna a shekarar 2015.
Ya yi aiki a Banki inda daga nan ya zama babban Darakta kuma ya zama mai rikon Manajan darakta na hukumar buga takardun sirri na Gwamnatin tarayya.
Ya kuma yi aiki a hukumar gudanarwar babban birnin tarayyar Abuja inda daga bisani ya zama shugaban sashen hulda da jama’a na kamfanin Mtel, kamafanin wayar sadarwa na NITEL
 An haife shi a shekarar 1966, Alhaji Bamalli ya yi karatun zama Lauya a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya na da digiri na biyu a kan huldar kasa da kasa da kuma aikin jakadanci da kuma Difiloma a kan harkar harkar shugabanci da ya samu daga jami’ar OXford kuma shi mabiyi ne a batun samun sasanci da ya samu daga jami’ar York, ta kasar Ingila.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.