Home / Big News / Zamu Rike Dukkan Gidajen Sarauta Bisa Amana – Sarkin Zazzau

Zamu Rike Dukkan Gidajen Sarauta Bisa Amana – Sarkin Zazzau

Zamu Rike Dukkan Gidajen Sarauta Bisa Amana – Sarkin Zazzau

Mustapha Imrana Abdullahi
Sabon Sarkin Zazzau mai martaba Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya bayyana cewa zai ci gaba da rikon daukacin gidajen da suka hadu suka yi sarautar Zazzau bisa gaskiya da amana 
Mai martaba Sarkin Zazzau ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta Muryar Amurka sashen hausa, inda ya ce shi a duk burinsa shi ne mahaifinsa ya yi Sarautar Zazzau amma cikin ikon Allah sai gashi Sarautar ta fado a kansa wanda hakan hukuncin Allah ne.
“Dukkan gidajen Sarautar Zazzau ai abu daya ne domin gidan Barebari Kakanni na ne su kuma gidan katsinawa akwai auratayya wanda matata daga gidan ne don haka zamu tabbata mun rike kowa da adalci”.
Sabon Sarkin ya kuma yi godiya ga Allah madaukakin Sarki da ya bashi ikon ganin wannan rana ta farin ciki.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.