Home / Lafiya / Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rufe Asibitin Zango 

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rufe Asibitin Zango 

Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna ta rufe asibitin Zango mai suna “Zango Islamic Clinic  and Maternity Home” saboda suna gudanar da aiki ba tare da izinin hukuma ba.
Shi dai wannan asibitin na nan ne a kan titin Zango a unguwar Tudun wada kaduna a karamar hukumar Kaduna ta Kudu, wadansu jami’an ma’aikatar lafiya ne tare da hadin Gwiwar wani kwamitin kula da harkokin lafiya da kuma kwamitin ma’aikatan Jinya da Unguwar Zoma sula gudanar da aikin tufe asibitin.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan an rufe wurin Daraktan ma’aikatan kula da masu haihuwa da Unguwar Zoma na ma’aikatar lafiya ta Jihar Kaduna, Salihatu Aminu, ta ce akwai wata tallar da aka Sanya wa da ya karade ko ina da ina a kafafen Sada zumunta inda ake kiran dukkan masu son a horar da su masu aikin kula da haihuwa da kuma masu karbar haihuwa na gargajiya a shekara daya.
” Wannan ne yasa hankalinmu ya karkata a kan wannan tallar a ranar 20 ha watan Agusta 2020 da kuma 21 ga watan Agusta 2020 sai muka je asibitin amma bamu ga komai ba mai kama da makarantar horar da masu Unguwar Zoma sai dai kawai wani ginin da ake amfani da shi a matsayin asibiti.
“A cikin asibitin akwai dakin haihuwa, wurin yi wa marasa lafiya tiyata, Maza da Mata dukkansu kuma marasa ingancin da suka cika ka’ida.
“Hatta su ka su ma’aikatan da muka gani a wurin ba su cancanci yin aikin ba amma suna bayyana kansu a matsayin masu aikin Unguwar Zoma da Likitoci”.
” Don haka ya zama wajibi kawai mu rufe wurin domin bamu da zabi” inji ta.
Daraktar ta kuma yi kira ga jama’a da su guji zuwa irin wadannan asibitoci saboda ba su da dukkan abubuwan da suka cancanci yin aiki wanda ya kasance hadari ne a rayuwar dan adam.
Sakatariyar ma’aikatan Unguwar Zoma ta kasa reshen Jihar Kaduna Kwamared Christiana Bawa cewa ta yi hedikwatar su ta kasa ce ta ankarar da su a kan wannan tallar da yake yadawa a kafafen Sada zumunta na zamani, suna tambayar cewa ta yaya za a iya kammala karatun horaswa na tsawon shekaru uku zuwa biyar amma wani ya ce zai kammala shi a tsawon shekara daya rak.
” Mun tuntubi ma’aikatar lafiya kuma bincike  ya nuna cewa babu wani abu mai kama da makaranta a wannan adireshin da kuma tallar da suka rika bazawa amma sun ce ma wurin karamin asibiti”.
” Da akwai dokokinnkafa asibiti da kuma kafa makarantar horar da ma aikatan lafiya da Unguwar Zoma dole ne kuma sai an bi dokokin nan kamar yadda ya dace.
” Muna son kiyaye lafiyar jama’ar Zango ne da ake cutar da su ta hanyar sama masu tsarin kula da lafiya mara inganci kuma wanda bai dace ba a wannan asibiti mara rajista keyi”. Inji ta
Sakataren mai kula da wuraren kula da lafiya masu zaman kansu Aliyu Bala Shehu ya ce hakika wannan asibiti ma Zango ya karya dokar ka ida a wurin kafa asibiti a kuma ci gaba da gudanar da ayyuka.
Ya gargadi jama’a da su guji zuwa dukkan wuraren da hukuma b ata tantance su ba dominnkamar yadda ya bayyana akwai wuraren da gidajen mutuwa ne kawai don haka dole a gujesu baki daya.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.