Home / Big News / Gwamnatin Jihar Sakkwato Na Kokarin Magance Matsalar Cutar Da Ta Bulla – Tambuwal

Gwamnatin Jihar Sakkwato Na Kokarin Magance Matsalar Cutar Da Ta Bulla – Tambuwal

Gwamnatin Jihar Sakkwato Na Kokarin Magance Matsalar Cutar Da Ta Bulla – Tambuwal
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, CFR Mutawallen Sakkwato ya bayyana cewa a madadin Gwamnati da kuma daukacin al’ummar Jihar, yana bayyana bakin cikinsa da jajantawa iyalai da yan uwan wadanda suka rasa ransu daga cikin al’ummar Jihar sakamakon cutar da ta bulla a unguwar Helele a cikin garin Sakkwato.
Cewa Gwamnati ta samu bayanin cutar da ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane hudu, mutane uku a nan cikin kwaryar unguwar Helele guda daya kuma bayan an kwantar da shi a asibiti. Guda Ashirin da hudu kuma suna asibiti ana duba lafiyarsu a wuraren kula da lafiya daban daban a Sakkwato.
Gwamnatin Jihar ta Sanya wani kwamitin kwararru, karkashin jagorancin kwamishinan lafiya da kuma na kula da Muhalli, domin su bincika abin da ya kawo wannan cuta da kuma samo hanyar magance ta.
Gwamnan ya kara da cewa a cikin wata takardar da ya sanyawa hannu cewa, Gwamnati ta dauki nauyin yi wa dukkan mutanen da ake duba lafiyar a asibiti magani kyauta kuma ana fatan samun lafiyarsu cikin Sauri su koma cikin iyalansu da masoyansu.
Mai girma Honarabul Aminu Waziri Tambiwal yana shawartar jama’a da su ci gaba da zama lafiya, ya kuma fadakar da su su rungumi kokarin tsaftace muhalli da kuma yin addu’o’in neman sauki daga Allah a wannan lokacin kalubale da ake samun jarabawa daga Allah.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa wadanda suka rasa rayukansu sakamakon dukkan rashin lafiya da kuma sauran abin da ya haifar da hakan, ya kuma bayar da sauki ga wadanda suka kamu da rashin lafiyar ya kuma ba mu kariya baki daya, na abin da muka Sani da wanda ba mu Sani ba.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.