Home / Uncategorized / Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Jajirce Domin Magance Matsalar Dalibai Ta Jami’ar Cyprus

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Jajirce Domin Magance Matsalar Dalibai Ta Jami’ar Cyprus

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 Gwamna Dauda Lawal ya karɓi jagoranci daga  gwamnatin da ta kasa biyan kuɗaɗen jarabawar ɗalibai har na shekaru uku, wanda hakan ya kange ɗaliban jihar Zamfara daga ɗaukar jarabawar  WASSCE da na NECO.
Matsalolin Rashin biyan kuɗaɗen karatu na makarantu daban-daban na ɗaliban jihar Zamfara da ke karatu a Cyprus da India, suna daga cikin ɗimbin matsalolin da wannan gwamnati ta gada daga gwamnatin da ta gabata.
Game da ɗaliban da ke karatu India da Sudan, gwamnatin jihar Zamfara ta shirya da jami’o’in da  Zamfarawan ke kataru a Indiya har sun kammala karatun su, yanzu haka ma suna shirye-shiryen dawowa gida.
Sakamakon yaƙin da ake yi a Sudan, yanzu haka an samu nasarar kwaso ɗaliban Zamfara 66. Amma kuma 14 daga cikinsu, masu karatun Nas-nas, ba su samu samar ɗaukar jarabawar ƙarshe ba. Gwamnatin jihar Zamfara, tare da haɗin gwiwa da Jami’ar Sudan, ta shirya wa ɗaliban 14 jarabawa a wata cibiyar da ba ta Jami’ar ba a nan Nijeriya. Gwamnatinmu ta ɗauki nauyin kuɗin jirgi, wurin kwana da abinci na Malamai uku daga Sudan da suka gudanar da jarabawar ɗaliban 14. Dukkan ɗaliban 14 sun zana jarabawarsu ta ƙarshe, sauran ɗaliban 52 kuma gwamnati ta ɗauki nauyin su a wasu Jami’o’i a Nijeriya.
Mun kafa tarihi ta hanyar warware irin waɗannan matsalolin da ɗaliban Zamfara suka fuskanta a Indiya da Sudan ta hanyar shiga tsakanin na gwamnatin jiha. Tambayar ita ce: Me ya sa Jami’ar Ƙasa da Ƙasa ta Cyprus ta bambanta?
Duk da ɗimbim matsalolin da aka samu a lokacin da aka tura ɗalibai zuwa Cyprus da wasu ƙasashe, gwamnatin jihar na bin dukkanin hanyoyin da suka dace don magance matsalar, amma mahukuntan makarantar na daƙile yunƙurin.
A ranar 12 ga Nuwamba, 2023, gwamnatin jihar ta biya jami’ar Naira Miliyan 84.7. Bayan kwana biyu, a ranar 14 ga Nuwamba, 2023, an sake tura Naira Miliyan 30.9 zuwa makarantar.
Jami’ar ƙasa da ƙasa ta Cyprus ta ci gaba da yin watsi da buƙatar gwamnatin jihar na aikewa da tawaga domin tattauna batutuwan da suka shafi ɗaliban mu da ake ba su tallafin karatu. Don haka sai da gwamnatin jihar ta tuntubi ofishin jakadancin Nijeriya da ke Turkiyya domin neman taimako.
A watan Mayun 2024, bayan gagarumin matsin lamba daga Ofishin Jakadancin Nijeriya na Ƙasashen Waje a Turkiyya, hukumomin makarantar sun sanar da gwamnatin jihar cewa, a shirye suke su karɓi tawaga a jami’ar da ke Cyprus, dangane da miƙa kuɗaɗe don nuna cewa da gaske ta ke. Sakamakon haka, a ranar 4 ga Yuni, 2024, gwamnatin jihar ta aika da Naira miliyan 100 kamar yadda jami’ar ta buƙata.
Dangane da haka ne Gwamna Dauda Lawal ya kafa wata tawaga mai mutane uku domin tafiya Jami’ar Cyprus. Tawagar ta haɗa da Mallam Wadatau Madawaki, Kwamishinan Ilimi, Kimiya da Fasaha; Bello Mohammed Auta, Kwamishinan Kuɗi; da Barau Muazu, Mai Bai Wa Gwamna Shawara na Musamman Kan Harkokin Kuɗi da Tattalin Arziki.
Tawagar ta na da alhakin tabbatar da haƙiƙanin adadin kuɗaɗen da jihar Zamfara ke bin jami’ar dangane da ɗalibai 93 da aka tura tallafin karatu tun daga shekarar 2019; a tantance dukkan ɗaliban jihar Zamfara da ke jami’ar da kansu don sanin haƙiƙanin adadinsu; don tabbatar da irin kwasa-kwasan da ɗalibai ke ɗauka, don tabbatar da shekarar kammala karatun kowane ɗalibi.
Sauran ayyukan sun haɗa da ganowa da tantance yanayin da ake gudanar da karatun, halin da gidajen kwanan ɗaliban suke, ciyarwa da sauran abubuwan da suka danganci ilmantarwa da samar da ababen more rayuwa, da samar da yarjejeniyar fahimtar juna don daidaita al’amura.
Kafin barin Nijeriya, tawagar ta tuntubi ofishin jakadancin Nijeriya da ke ƙasar Turkiyya, wanda hakan ya sa wasu jami’an ofishin guda biyu suka shiga tawagar zuwa ƙasar Cyprus a ranar 14 ga Agusta, 2024, domin kammala ayyuka da aka lissafa a sama. A ranar 15 ga watan Agusta, sun gana da ɗaliban da kuma Hukumar Gudanarwar Jami’ar, inda suka warware matsalar
Ganawar farko da hukumar ta yi da Farfesa Majid, tawagar ta buƙaci a aiwatar da duk wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Jami’ar Cyprus da Gwamnatin Jihar Zamfara, wanda ya haɗa da; jimillar bashin da ake bin kowane ɗalibi daga farko har zuwa yau, wanda ƙunshi adadin kuɗin da ake bi a kowane zangon karatu, kuɗaɗen da aka fara biyan da raguwar kuɗaɗen; jimlar karatun ɗalibai a kowane zangon karatu tare da ranar kammala karatun ɗaliban da suka biya kuɗin da kansu don guje wa tsayawar zangon karatu, adadin da aka biya wa kowane ɗalibi da jimillar duka kuɗaɗen.
A ganawar da ta yi da shugaban jami’ar Farfesa Habil Nadiri, tawagar ta gabatar da batutuwa da dama da ɗaliban jami’ar ke fuskanta, waɗanda suka haɗa da rashin rijistar ɗalibai domin ba su damar halartar laccoci da kuma samun kayayyakin makaranta don gudanar da karatunsu yadda ya dace; korar ɗaliban gaba ɗaya (sai dai mata goma) waɗanda ke maneji a ɗakin kwanan ɗalibai maza na makarantar; hana dukkan ɗalibai (ciki har da mata goma) abinci daga wurin cin abincin makarantar tun ranar da aka kore su daga ɗakin kwanan ɗalibai.
Sauran batutuwan da aka gabatar wa mahukuntan makarantar sun haɗa da sanya wa ɗaliban jihar Zamfara laƙabi da “a ƙarƙashin dokar korar ɗaliban,” wanda aka koka da shi a matsayin hukunci mai tsauri tun da ba su yi wani laifi ga jami’a ko ƙasa ba, da kuma korar ɗaya daga cikin ɗaliban ba tare da sanar da gwamnatin jihar Zamfara ko ofishin jakadancin Njjeriya da ke Ankara ba. Mun kuma yi tir da wannan matakin da aka aiwatar ba gaira ba dalili.
Tawagar Zamfara ta bankaɗo rashin daidaito a jami’ar Cyprus. Ofishin babban sakataren ya bai wa gwamnati Yuro 947,544.71 a matsayin jimillar kuɗaɗen da jami’ar ke bin Jihar Zamfara.
Ofishin babban mai ba da shawara ga kwamitin amintattu kuma shugaban Sashen Habaka  Al’amuran Ƙasa da Ƙasa ya ba da jimillar basussukan da ake bin jihar ke bi kamar Yuro 650,730.24.
Ofishin Harkokin Ƙasa da Ƙasa ya tabbatar da cewa ofishin Babban Sakatare bai sabunta tsarinsa ba tare da biyan kuɗi da yawa. Mun yi nazari kan jimillar adadin da ofishin kula da harkokin ƙasa da ƙasa ya bayar kuma mun gano wasu matsaloli da dama da ya kamata a gyara, wanda hakan ya ƙara rage yawan basussuka.
Tun bayan dawowar tawagar, gwamnatin jihar Zamfara ta daɗe tana jiran saƙo daga jami’ar Cyprus dangane da adadin kuɗaɗen da ake buƙata domin kawo ƙarshen wannan ka-ce-na-ce.
Ofishin Jakadancin Nijeriya a Ankara ya yi aiki tuƙuru don ƙarfafa Ofishin Jakadancin Cyprus don matsa wa Jami’ar Cyprus don samun takardun hukuma. Muna fatan wannan shiga tsakani na diflomasiyya zai taimaka wajen tilasta wa jami’ar yin abin da ya dace ba tare da wata matsala ba.

About andiya

Check Also

Dangote Hails Tinubu on Impact of Crude for Naira Swap Deal

      …As Dangote Refinery partners MRS to sell PMS at N935 per litre …

Leave a Reply

Your email address will not be published.