Home / Lafiya / Gwamnatin Yobe Ta Amince Da Sanya Fitilun Kan Hanya

Gwamnatin Yobe Ta Amince Da Sanya Fitilun Kan Hanya

 

 

 

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Majalisar zartaswar jihar Yobe ta amince da kashe Naira biliyan 3,129,608,370,00 don saye da kuma sanya fitilun masu amfani da hasken rana,  guda 2,880 a manyan garuruwa biyar na jihar.

Kwamishinan ma’aikatar yada labarai da  harkokin cikin gida da al’adu na jihar Yobe, Alhaji Muhammad Lamin ne ya sanar da hakan, yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin Jihar  dake Damaturu.

 

Kwamishinan ya bayyana cewa manyan garuruwan da za su ci gajiyar sanya fitulun hasken rana su ne;  garuruwa  Buni-Yadi, Gashua, Geidam, Nguru da Potiskum.

A cewarsa, bayan batutuwa da dama da majalisar zartaswar jihar ta tattauna kan su, sun amince da gudanar da wasu muhimman ayyukan raya kasa da suke da muhimmanci ga al’ummar jihar.

 

Kwamishinan ya kara da cewa, sauran ayyukan da aka amince da su sun hada da kwangilar siyan motocin Toyota Camry 2020 guda 10 da Toyota Prado Jeep V8 guda 2, samfurin 2021 ga alkalan babbar kotuna da kuma Khadis na kotun daukaka kara ta Shari’a a kan kudin.  N531,000,000.00.

 

Ya bayyana cewa majalisar ta kuma amince da siyan motocin Toyota Hilux guda 3 kan Jimlar kudin N131,549,133.50, tare da  sayan mota kirar Toyota Hiace Bus guda 1 da mota kirar Toyota Hilux 2020 guda 2 da Toyota Prado Jeep guda 1, samfurin 2022 akan kudi N215,000,000,00:

“Majalisar zartaswar ta kuma amince da kwangilar siyan mota kirar Land Cruser Armored Prado V8 VXL Jeep 2022 Unit 1 akan kudi N149,425,000.00.

 

 

“An amince da siyan mota guda 1 Toyota Land Cruiser Jeep V8 Bullet Proof VIF zuwa sashin Protocol na Gidan Gwamnati akan kudi N146,600,000.00

“Majalisar ta kuma amince da siyan mota kirar Toyota 18 Seater Bus guda 2, Prado Jeep guda 1 da Toyota Hilux guda daya zuwa ofisoshin jihar (Liaison offices) dake garuruwan Maiduguri, Kaduna da Abuja kan kudi N210,470,711.20 da sauran manyan ayyuka da majalisar ta amince da su”.  , in ji kwamishinan.

 

 

Tun da farko a wajen taron majalisar zartaswar, kungiyoyi daban-daban sun ba Gwamna Mai Mala Buni lambar yabo bisa nasarorin da ya samu a jihar, lamarin da ya tabbatar da maganar cewa Gwamna Buni na kokarin kawo sauyi a jihar ta Yobe ta fuskoki dabam-dabam na cigaba.

About andiya

Check Also

Northern Christian Leaders Pay Homage to Khalifah Sanusi, Strengthening Ties.

Northern Nigerian Christian Clerics Pay Homage to His Highness Khalifah Sanusi Lamido Sanusi to Strengthen …

Leave a Reply

Your email address will not be published.