Daga Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta fara aikin sabunta birane kashi na daya a babban birnin jihar.
Kashi na daya na aikin na garin shi ne hanyar da ta hada gidan gwamnati da titin Bello Bara’u, titin Tankin Ruwa, da tsohuwar hanyar kasuwa, da zagayen ofishin ‘yan sanda da dai sauransu.
Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar ne a zauren majalisar gidan Gwamnatin Jihar da ke Gusau.
Ya kara da cewa, samar da ababen more rayuwa wani bangare ne na kudirin Gwamnatin Jiha na sabunta birane, da nufin samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa su bunkasa da samun saukin rayuwa.
Sanarwar ta kara da cewa: “Gwamnatin Jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani katafaren kamfanin gine-gine, Ronchess Nigeria Limited domin fara shirin sabunta birane a jihar.
“Gwamna Lawal ya nanata kudirin Gwamnatin sa na ganin an dawo da rugujewar ababen more rayuwa ta hanyar sake gina sabbi da kuma gyara tsofaffin da suka fara daga Babban Birnin Jiha.
“Sabuntawa a biranen da aka fara da titunan gari a babban birnin tarayya, Gusau, shi ne mafarin samar da ababen more rayuwa da za su mamaye dukkan kananan hukumomin jihar.
“Rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar yana nuna cewa Gwamnatin Jihar Zamfara ta fara wani aiki da zai sauya labari zuwa ga kyau.
“Gwamnati za ta samu nasarori da dama tare da hadin kan mutanen kirki na jihar Zamfara. Sabunta birni yana ɗaya daga cikin dabarun da aka yi amfani da su don aiwatar da aikin ceto.”
Da yake mayar da jawabi a madadin kamfanin gine-ginen, babban daraktan kamfanin na Ronchess, Samson David ya bayyana cewa suna son yin aiki mai kyau a birnin Gusau yadda suka yi a jihar Kaduna.
Ya kuma yabawa gwamnatin jihar Zamfara da ta same su da suka cancanci a ba su kwangilar tare da bada tabbacin za su gudanar da ayyukan.