Related Articles
Imrana Abdullahi
Tsohon shugaban majalisar wakilai ta tarayya Alhaji Ghali Umar Na’Abba, ya bayyana Gwamnoni a tarayyar Najeriya a matsayin wadanda suka kashe tsari da tanaje – tanajen Dimokuradiyya a Najeriya.
Alhaji Umar Na’Abba, ya ce sakamakon son zuciyar da Gwamnonin ke nuna wa ne ya sa babu wata Dimokuradiyya da ake yi a halin yanzu musamman a cikin jam’iyyun siyasa.
Ghali ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo lokacin da ya tattauna da kafar bbc.
“Saboda in dai kana bukatar tsayawa takara ko zama wani abu a cikin jam’iyya dole sai dai ka kasance yaron Gwamna ne ko kuma ka Sanya kudi ka sayi duk wata kujerar da Keke bukatar tsayawa takara a cikin jam’iyyar da Gwamnan ya kasance a ciki in kuwa ba haka ba sai dai ka hakura kawai, akwai tsari irin na kudanyya da Juna a tsakanin yayan jam’iyya da kuma tarurruka a matakai daban daban tun da aka kashe wannan sai ya zama babu maganar Dimokuradiyya a cikin jam’iyyu sai komai ya koma a hannun Gwamnoni kawai”, inji Ghali.
Ya ci gaba da cewa “Ni ba za a hada kai dani ayi zumunci ba, ko a lokacin muna majalisar wakilai domin irin yadda ta rika kasancewa tsakanin mu da Obasanjo ya na shugaban kasa, sai ya hada kai da Gwamnan Kano na wancan lokacin da yakasance abokin tafiyar Obasanjo aka bayyana sakamakon zabe na cewa wai na fadi, saboda duk Najeriya a lokacin zabe na aka fara fadi tun daga wancan lokacin aka ci gaba da yin rashin Dimokuradiyya a zaben Najeriya abin da Gwamna yake bukata shi ake aiwatarwa kawai a koda yaushe”.
Saboda haka ne nake tabbatarwa jama’a cewa babu Dimokuradiyya a tare da Gwamnoni kuma sun kashe tsarin Dimokuradiyya sai na su tsarin kawai ake bi musamman a cikin jam’iyyu.
Ghali Na’ABBA ya kara da cewa saboda rashin Dimokuradiyyar da ke faruwa a Najeriya da ya haifar da rashin ingancin jam’iyyu, a halin yanzu ba na cikin kowace jam’iyya kowa ya san na yi PDP na zama shugaban majalisar wakilai a karkashinta kuma na barta na koma APC hakika nan ma na fice don haka a yanzu ba ni da wata jam’iyya”, inji Ghali Umar.