Home / KUNGIYOYI / HAJIYA DOKTA AMINATOU ABDOULKARIM GARKUWAR MARAYU DA MARASA GALIHU

HAJIYA DOKTA AMINATOU ABDOULKARIM GARKUWAR MARAYU DA MARASA GALIHU

 

….Ta na Kulawa da gidajen marayu Sama da dari Bakwai

 

DAGA IMRANA ABDULLAHI

 

AN bayyana Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad a matsayin Garkuwar Marayu da marasa Galihu da kuma duk masu karamin karfin da ke neman a tallafa masu.

Yayan kungiyar “A A Charity Foundation”, da ke fafutukar kokarin inganta rayuwar Marayu da marasa galihu da suke a tarayyar Najeriya ne suka bayyana hakan.

Alhaji Abdullahi Iliyasu shugaban yan Nijar na Gwale a cikin Jihar Kano ya ce shi ne ke rike da tafiyar Hajiya Aminatou Abdoulkarim Muhammad, don haka sun tabbatar da jaruntakar wannan Bawar Allah saboda duk duniya ta san da hakan.

Abdullahi Iliyasu ya ci gaba da cewa a duk wata Dokta Aminatou na kulawa da gidajen da marayu suke sama da dari 700.

Iliyasu ya kara da cewa ayyukan da wannan Baiwar Allah ke aiwatarwa ba su Lissafuwa ko a cikin Jihar Kano balantana kuma a Najeriya baki daya.

Ya ce saboda ” komai Dare idan na gayawa Hajiya Dokta Aminatou ga gidan marayu can kuma ga halin da suke ciki nan take za ta kawo masu dauki da abin hannunta ta tallafa masu domin su fita daga halin da suke ciki rayuwarsu ta inganta”, Inji Iliyasu.

Kai za a iya cewa Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad a kullum sai ta yi aikin sadakatujjariya ta fuskar inganta rayuwar jama’a a wurare daban daban, a bisa hakan ne muke fata a koda yaushe Allah ya kama mata.

A bisa wani kwarya kwaryan binciken da muka yi mun tabbatar da cewa ruwa ko Nisan wuri ba zai hana Dokta Aminatou ta shiga lungu da sako ba domin zakulowa da taimakawa jama’a Talakawa masu neman a tallafasu a harkar rayuwar yau da kullum.

“Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad na shiga kauyukan da ke cikin Daji ta zakulo jama’ar da suke cikin surkunin Daji ta kuma tallafa masu, ta na shiga ta zauna da su ba tare da nuna kyama ko wani ganin fifiko ba, ta tattauna da su ta ga wane tallafin ya dace da su daga farko? Kuma hakan za a yi, sai ta fadakar da su a kan abin da ya dace ta fuskar ilimi, sana’o’i da samun zaman lafiya a tsakanin jama’a. Zaka ganta a cikin kungurmin Daji ko a Rugagen Fulani da kauyuka masu nisa ta shiga wurin jama’a Talakawa domin ta karfafesu, wanda hakan ne ma ya sa kasarta ta jamhuriyar Nijar da ake neman wanda zai yi aikin da a shekaru sama da Goma aka kasa samun wanda zai yi ita aka nemo kuma a halin yanzu kwalliya ta biya kudin sabulu”.

” Kai hatta gidanta na Abuja da kuma duk inda take nan da nan zaka ga jama’a suna tururuwa kafin ka ce me, mama’s ce zaka gani ko ina domin irin kyakkyawar zuciyarta da kuma kyauta da taimakon marasa karfi.

Kamar yadda ita da kanta take fadi “koda na tashi ba ni da shi amma indai hidimar jama’a ce sai kaga nan da nan kawai Allah ya kawo jama’a sun samu don haka ba abin da zan ce ma Allah madaukakin Sarki sai dai godiya”, inji Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad.

A bayanan da muka samu cewa Gwamnatin kasar Nijar na son samun wanda zai yi aikin nemo yan asalin kasar Nijar da ke a cikin Najeriya, sai aka cewa Gwamnati sai Hajiya Aminatou ce za ta yi wannan aikin a samu abin da ake nema. An yi tsawon shekaru sama da Goma ana son a samu yawan mutanen da ke Najeriya yan asalin kasar Nijar amma ba a samun yawan mutanen, domin ana son a samu dan majalisar kasar Nijar daga Najeriya kamar yadda ake da su a wadansu wurare”.

“Amma tun da aka lallashi Hajiya Dokta Aminatou Abdoukarim Muhammad, ta kuma amince da za ta yi aikin kwakulo mutanen a duk inda suke a birane da karkarun Najeriya baki daya nan da nan sai aka samu fiye ma da abin da ake nema ko saran samu, saboda an yi wa jama’a rajistar da za ta ba su damar su kada kuri’a idan zaben dan majalisar dokokin kasar Nijar yazo. Kuma a haka ma akwai wata Jiha da kuma wuraren da ba ayi aikin rajistar masu zaben ba, amma duk da hakan a wuraren da aka gudanar da aikin an samu fiye da abin da ake saran samu duk da Injunan rajista ma ba su wadaci aikin ba, wanda sakamakon hakan akwai ninkin ba ninkin yawan alkalumman da aka samu da ba a yi masu rajistar ba ma sam”.

Kuma nasarar nan ta samu ne sakamakon jajircewar da Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhamamd ta yi ta yin aiki da dukiyarta, karfinta, jinin jikinta da duk wata damar da take da ita wajen kwakulo jama’ar birni da karkara a duk inda suke a fadin Najeriya domin ko’ina ta na da mutane.

Kai wannan Baiwar Allah idan an yin hidima a gidanta zaka ga da kanta take rabon abincin da jama’a za su ci kuma duk aikin da za a yi itama tare da ita ake yi ba tare da gajiya wa ba, ha aiki da kudinta ha kuma aiki da karfi da jinin jikinta tare da aikin da dimbin tunani da kaifin basirar da Allah ya yi mata domin idan ka yi magana da uta ka san lallai ta na da kaifin basira sosai.

About andiya

Check Also

Aliyu Sokoto tasks cabinet on transformation drive, ‘ be committed and sincere 

  By Suleiman Adamu, Sokoto SOKOTO state Governor Dr Ahmed Aliyu Sokoto has tasked members …

Leave a Reply

Your email address will not be published.