…Zan Yi Amfani Da Albashina In Sayo Wa Mata Kayan Sana’a – Sa’adatu.
A kokarin ganin rayuwar mata da kananan yara da inganta Babbar Kwamishar Kidaya ta Najeriya Hajiya Sa’adatu Garba Dogon bauchi ta Sadaukar da Albashinta na Shekara guda ga Matan Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu.
Babbar Kwamishinar ta Bayyana Haka ne a lokacin da take raba Buhunan shinkafa kimanin guda Dubu Uku ga al’Umar Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna.
Ta ce za ta tara Albashinta ta sayo kayayyakin Sana’oi ta raba ga Mata domin dogaro da kawunansu.
Mutanen da suka amfana da rabon abinci da tayi sun nuna farinciki tare da yin addu’oi a gare ta, mutanen da suka amfana da rabon da tayi sun hada da Maza, Mata da masu buqata ta musamman.
Tabbas idan mutane masu rike da mukami suna tallafawa al’umma irin haka za’a samu sauki ta fannoni da dama
Hajiya Sa’adatu Garba Dogonbauchi muna addu’ar Allah ya yi miki sakayya da Gidan Aljanna ya kara kai Matsayi gaba.