Home / News / Hatta Wayar Hannunmu Sai Da Aka Kwace – James Bawa Magaji

Hatta Wayar Hannunmu Sai Da Aka Kwace – James Bawa Magaji

Hatta Wayar Hannunmu Sai Da Aka Kwace – James Bawa Magaji

Mustapha Imrana Abdullahi
Tsohon Mataimakin  Gwamnan Jihar Kaduna Mista James Bawa Magaji ya bayyana cewa a lokacin da za su fita daga gidan Gwamnati hatta wayoyinsu na hannu da aka ba su domin yin aiki sai da aka karbe.
Tsohon Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
James Bawa Magaji ya ce sabanin irin yadda lamarin ke faruwa a halin yanzu su a zamaninsu zaka ga mutane na zuwa daga kauyuka wasu ma ba su da ko Takalmi a kafafuwansu amma kuma suna shiga har gidan Gwamnatin Jiha.
“Da farko dai wasu idan sun zo sai a hana su shiga cikin gidan Gwamnati amma sai da muka kira hankalin masu hana su muka gaya masu a rabu da su, saboda wadansu daga cikinsu an ci zabe ne daga kuri’un da suka bayar a kauyukansu don haka a bar kowa ya shiga gidan Gwamnati sai mu ne kawai muke da ikon ganin duk wanda zamu gani”.
Ya kuma yi kiran cewa yana da kyau matuka a raba siyasa da kashe irin makudan kudin da ake kashe wa kafin a zabi dan takara, saboda idan mutum ya bayar da kudi kamar zai sayi mutane ya biya idan ya hau ba zai yi wa kowa aiki ba balantana ganin darajar jama’a.
James Bawa Magaji, ya ce “a lokacin muna Gwamnati ina matsayin mataimakin Gwamnan Kaduna aka tattauna a matakin Gwamnatin Jiha inda aka yanke hukuncin a kai wa Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa motocin hawa da direbobi gidansa domin gudanar da aikin yau da kullum amma ana kai masa nan da nan ya ce a mayar sai dai ya dauki wata mota karama ya sayar itama ya aiwatar da gyaran katangar gidansa, shi kenan haka aka yi”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.