Home / Labarai / An Sace Malamin Makaranta, Yara Biyu, An Yi wa 1 Rauni A Zariya

An Sace Malamin Makaranta, Yara Biyu, An Yi wa 1 Rauni A Zariya

An Sace Malamin Makaranta, Yara Biyu, An Jiwa 1 Rauni A Zariya
 Imrana Abdullahi

Bayanan da muke samu daga garin Zariya na cewa wadansu yan bindiga da ya zuwa yanzu ba a san ko su wanene ba sun sace wani babban Malamin makarantar Nuhu Bamalli Injiniya Bello Atiku da yara biyu na Sanusi Hassan da kuma wani ma’aikaci a makarantar da ba Malamin makaranta ba.

Wannan lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 9 na Yamma a wurin gidajen masu aiki a makarantar.
Mahaifin Yaran da aka dauke a halin yanzu yana asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya  ana duba lafiyarsa sakamakon irin raunukan da ya samu daga harbin Bindiga

Baki dayan Malamin makarantar da kuma ma’aikacin da ba Malami ba makwabta ne da ke a layin Aliyu unguwar Tudun Wada Zariya.

 

Jami’in da ke hulda da jama’a a rundunar Yan Sanda ta kasa a Jihar Kaduna ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar abin da ya faru a makarantar Nuhu Bamalli.

Ya ce tuni aka fara gudanar da bincike a kan lamarin domin a kubutar da wadanda aka kwashe.

Ya shawarci mazauna wannan makaranta da su ci gaba da zama cikin natsuwa musamman ganin ana ta kokarin samo inda mutanen da aka kwashe suke domin kubutar da su.

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.