Home / Lafiya / HUKUMAR UNICEF ZA TA ZUBA JARI A JIHAR ZAMFARA 

HUKUMAR UNICEF ZA TA ZUBA JARI A JIHAR ZAMFARA 

Daga Imrana Abdullahi

BIYO BAYAN IRIN KOKARIN DA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA KEYI NA GANIN JIHAR TA SAMU ZAMA DA KAFAFUNTA YASA A YANZU HUKUMAR UNICEF TA AMINCE DA KARA ZUBA JARI DOMIN INGANTA AL’AMURAN LAFIYA, ILIMI DA KUMA CI GABAN MATA.

Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Dauda Lawal ya tabbatar wa da hukumar samun hadin kai da dukkan goyon bayan da ake bukata domin bukata ta biya nufi musamman a wadannan fannonin da aka ambata.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Nuhu Salihu Anka,Darakta Janar, na Gwamnan a kan harkokin kafafen yada labarai da sadarwa.

Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Dauda Lawal ya bayyana aniyar Gwamnatin da yake yi wa jagoranci tafuskar  ci gaba da hadin gwiwa da hukumar UNICEF musamman a bangaren kiwon lafiya da ilimi da kuma ci gaban mata.

Gwamna Lawal wanda ya karbi bakuncin tawagar UNICEF karkashin jagorancin Dokta Maryam Sa’id a gidan gwamnati da ke babbar birnin Jihar Gusau, ya ce gwamnatin jihar Zamfara ta ci gaba da jajircewa wajen hada gwiwa da kungiyoyin da za su bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar da al’ummarta baki daya.

Ya kara da cewa gwamnatin sa a shirye take ta biya takwaran ta kudaden ayyukan da za su shafi rayuwar al’umma, yana mai cewa UNICEF na bukatar kara yin aiki a jihar tare da bada tabbacin tsaro da tsaro a jihar Zamfara.

Gwamnan wanda ya godewa UNICEF bisa wannan ziyara, ya bukace su da su inganta alakar da kuma kyautata dangantaka, duba da irin mawuyacin halin da jihar ke ciki shekaru da dama da suka gabata, inda ya ce UNICEF na iya bakin kokarinta ga jihar wajen shawo kan matsalolin.

Da take jawabi tun da farko, shugabar tawagar UNICEF Dr. Maryam Sa’id ta jajanta wa gwamnatin jihar kan rashin tsaro da ya lakume rayuka da dama, inda ta ce a shirye suke su saka hannun jari tare da tallafa wa jihar domin samun ci gaba.

Ta bayyana shirin su na ci gaba da aiki da gwamnatin jihar Zamfara da kuma tabbatar da shirin raya jihar, inda ta bayyana cewa sun zuba jarin sama da naira biliyan biyu (N2b) a jihar a bara.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.