Home / Labarai / Ina Jiran Masu Zaben Sarki Su Aiko Da Sunayen Ne

Ina Jiran Masu Zaben Sarki Su Aiko Da Sunayen Ne

Ina Jiran Masu Zaben Sarki Su Aiko Da Sunayen Ne

 Imrana Abdullahi

GWAMNAN Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i ya fito fili ya bayyana cewa lallai ya lura mutane da dama sun zuba ido kan wanda zai zama sabon Sarkin Zazzau, kuma saboda haka yayi addu’a Allah ya baiwa masu zaben Sarki hikimar zaben Sarki mai irin halayya, aiki da  dabi’un marigayi Alhaji Shehu Idris tsohon Sarkin Zazzau.

Mai magana da yawun Gwamna El-Rufai, Mista Muyiwa Adekeye, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar  da ya fitar da  yammacin Larabar da ta gabata.

Sanarwar ta ce, “Tun da an kammala kwanakin makoki, gwamnatin jihar Kaduna na sauraro cikin ‘yan kwanaki masu zuwa a kawo mata shawarwarin masu zaben sarki a masarautar Zazzau game da sabon Sarki domin Gwamnati ta aiwatar da na ta aikin da ta saba domin jama’a.”

“Al’umma su saurari sanarwar gwamnati kuma su yi watsi da jita-jita da wasu ke yadawa, saboda wadansu mutane na ta yada labaran karya.”

Gwamna El- Rufa’I ya yi addu’ar Allah ya ba masu zaben Sarkin hikima da basirar zaben Sarkin da zai dace da abin da jama’a suke fatar samu.

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.