Home / Big News / INA KUDIN JAM’IYYAR APC NA JIHAR KATSINA?

INA KUDIN JAM’IYYAR APC NA JIHAR KATSINA?

 

Wani bincike da wannan jaridar ke yi akan jam’iyya mai mulki ta APC da yadda shugabannin ta na jiha ke tafiyar da ita, ya gano abubuwa masu daure kai da neman bayani a cikin tafiyar da shugabancinta.
Misali a yayin da shugaban ke rayuwa kamar wani sarkin kasar larabawa.wasu masu taimaka masa a matakin jaha,Bara suke yi.

Daga cikin binciken ne muka tsakuro wannan rahoton mai taken ina kudin jam’iyyar APC Katsina? Wanda nan gaba jaridun Taskar Labarai da the Links da kuma Katsina City News zasu fitar da cikakken rahoton abin da suka gano. Na kashin dankalin dake faruwa a shugabancin jam iyyar ta APC a jahar katsina.

Mun tsakuro wannan rahoton ne na ina kudin jam’iyyar ? Sakamakon munga yadda aka sai da fom na zaben cike gurbi a karamar hukumar Bakori wanda dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar ya rasu a wani lokaci da ya wuce.

Binciken mu ya gano cewa kusan duk shugabannin jam’iyyar ta APC dake jihar Katsina, ba wanda yasan ya aka yi da kudin kason jam’iyyar ta jiha wanda uwar jam’iyya ta kasa ta bata na sayar da fom din yan takara a zaben 2019.

Tsarin mulki na jam’iyyar APC ya tsara cewa duk kudin sayar da fom na uwar jam’iyya ne, amma zata baiwa reshen jam’iyya na jiha wani kaso.

Binciken mu ya gano jam’iyyar a matakin jiha ta sayar da fom da suka kama na duk zabubbukan da aka yi, kudin sun kai daruruwan miliyoyin nairori.

Kuma uwar jam’iyya ta ba reshen jam’iyya na jiha kasonta amma ba wanda ya san ya aka yi dasu, jaridun nan sun yi wani bincike a ofishin uwar jam’iyyar na kasa, wanda suka tabbatar mana da cewa duk sun biya jihohi baki daya abin da ya kamata a basu kamar yadda ka’ida ta tabbatar.

Uwar jam’iyyar ta tabbatar mana da cewa, hatta taimakon da ya kamata a baiwa jihohi duk ana basu, kuma jihar Katsina ita ce tafi amfana saboda da jihar shugaban kasa ce.

Jaridar nan mun tambayi da yawa daga cikin shugabannin jam’iyyar suka bamu amsa cikin amana cewa, ba wanda yasan komai akan kudin jam’iyya sai shugaban jam’iyya na jiha. Alhaji Shitu S Shitu.

Nawa gwamnatin jiha ke tallafawa ofishin Jam’iyya? Nawa ake kashewa? Babu Wanda ya sani a kashi casa’in na shugabannin jam’iyya na jiha da jaridun nan sukayi magana dasu bisa amana.
Nawa zababbu kan taimakawa jam iyyar, lokaci babu Wanda ya sani.a iya binciken mu.in banda mutum daya da yan koren shi.

Nawa aka tara gudummuwa nawa aka kashe a zaben 2019, babu mai iya baka wannan amsar duk a membobi ko shugabannin jam’iyya na jiha.

Kowa ka tambaya zai fada maka bisa amana cewa bai sani ba, amma a tuntubi uwar jam’iyya ta jiha.

Jam’iyyar tana da asusun ajiya na banki. Da binciken mu ya kai wajen asusun yana zama kamar azururu ne kawai a saka a kuma cire, hatta lokacin da muka samu bayanin abin dake cikin ajiyar bankin babu wani kudin kirki a ciki ya zuwa ranar 12/7/2020 lokacin da muka gano nawa ke a ciki?

Jaridar Taskar Labarai ta rubutu wasika ga shugaban jam’iyyar don jin ta bakin sa a ranar 27/7/2020, wanda sakataren gudanarwar Ofishin jam’iyyar ya bugo waya ya tabbatar da sun samu takardar, har ma ya nemi sanin adireshin ofishin jaridar koda zasu bada amsa.

Da muka ji shiru a ranar 5/8/ 2020 aka sake rubuta wata takardar domin tuni har zuwa rubuta rahoton nan 3/9/2020 babu amsa.

Muna fatan kafin mu saki cikakken rahoton namu zamu samu amsa daga wajen su. A rubuce ko ta sakon murya daga cikin bayanan da muke nema har da akan wani kamfani mai suna Marmara na wani shugaban jam’iyyar da ya samu kwangila har guda saba’in da takwas a wata hukuma a wata shekara, shin da sunan jam’iyya ne ko nasa ne? Da wasu batutuwa na zargin amfani da jam iyya ana azurta kai.da wasu shugabannin jam iyyar sun tsara mata Dan takarar gwamna a 2023.
……………………………………………………………………….
Taskar labarai jarida mai zaman kanta dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta.tana da yar uwarta ta turanci dake a www.thelinksnews.com. duk sako a aiko ga katsinaoffice@yahoo.com da whazzap 07043777779

About andiya

Check Also

Gwamnatin Hadin Kan Jama’a Na Haifar Mana Da Nasara – Gwamna Uba Sani

  …Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri Daga Imrana Abdullahi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.