Home / Labarai / Infoma Ya Fi Barayin Da Ke Cikin Daji Illa – Kabiru Charanchi

Infoma Ya Fi Barayin Da Ke Cikin Daji Illa – Kabiru Charanchi

Mai ba Gwamnan Jihar Katsina shawara a kan harkokin siyasa Honarabul Kabiru Sha’aibu, ya bayyana cewa masu tseguntawa barayin cikin daji da ke daukar mutane da aka fi sani da Infoma sun fi na cikin dakin Illa.
Kabiru Shu’aibu ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta Farin wata.
Shu’aibu ya ci gaba da cewa su masu tseguntawa na cikin daji bayanai a zo a dauki mutane sune masu Illa saboda sun san sirrin jama’a saboda haka ya dace asa idanu sosai domin bankado wadanda ke yin irin wannan mutum aikin.
“Gwamnatin Jihar Katsina na daukar matakai masu gauni kwarai a kan duk wani ko wasu da aka samu da irin wannan mummunan aikin a cikin al’umma.
‘Infoma ne zai tseguntawa masu daukar mutane cewa wane yana da kudi ko wani dan uwansa na da kudi don haka diana an dauke shi za a samu kudi”.
Sai ya yi kira ga al’umma su tashi tsaye game da batun duk wani da aka samu cikin mutane yana irin wannan mugun aiki na zaluntar wadanda ba su jiba ba su gani ba.
“Akwai wadansu wuraren da aka samu masu satar jama’a da a halin yanzu duk Gwamnati ta yi maganinsu baki daya son haka mutane su ci gaba da taimakawa Gwamnati”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.