Home / Labarai / Injiniyan Farko Da Ya Fara Shiga Rijiyar Ruwan Zam Zam Ya Rasu

Injiniyan Farko Da Ya Fara Shiga Rijiyar Ruwan Zam Zam Ya Rasu

Injiniyan Farko Da Ya Fara Shiga Rijiyar Ruwan Zam Zam Ya Rasu
Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar yadda zaku iya gani a wannan hoton shi ne mutum na farko da ya shiga rijiyar ruwan Zam Zam, wato injiniya Dokta Yahya Koshak, kamar yadda bayanai suka gabata shi dai wannan bawan Allah ya shiga cikin rijiyar ne domin gano asalin inda ruwan ke bubbugowa tun daga kasa.
Ya dai gano hakan ne domin tabbatar da yin gyara a lokacin Sarki Khalid a shekarar 1979, ya dai rasu ne a jiya a Saudiyya.
Kuma aikin yashe da ya yi shi ne mafi girma a tarihin rijiyar, kuma shi ne ya jagoranci sauran wadanda suka shiga rijiyar kusa da dakin Ka’bah.
Allah ya jikansa da rahama ya gafarta masa dukkan kura kuransa amin.

About andiya

Check Also

PDP NorthWest Youth Leader Condolences to Senator Garba Maidoki and the Emir of Yawuri In Kebbi State

      The Northwesr people’s Democratic party (PDP) Youth leader in the North-West Zone, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.