Home / Ilimi / Jahilci Ne Musabbabin Ta’addanci Da Kashe Kashe – Masari

Jahilci Ne Musabbabin Ta’addanci Da Kashe Kashe – Masari

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana jahilci da tsananin rashin ilimi a matsayin manyan dalilan da suke haifar da daukar ayyukan jama’a ba gaira ba dalili a cikin al’umma.
Masari ya bayyana hakan ne a wajen babban taron da aka shiryawa malaman Masallatan Juma’a na kwanaki biyu a katsina. Inda ya ce kashi 90 saga cikin dari na yan ta adda da ke zauna a cikin daji rashin ilimi ne da tsananin jahilci da ya yi masu kanta ke haifar da ta adda wanda hakan ya sabawa koyarwar addinin Islama.
“Duk da cewa masu aikata wannan kashe kashen suna cewa su musulmi ne amma ayyukansu ya saba wa koyarwar addinin Islama baki daya.
Masari ya yi magana a game da irin yadda aka kai harin kauyukan Tsauwa da Dankar a karamar hukumar Batsari da yan ta adda suka kai, ya bayyana irin yadda aka rika daukar kananan yara da ke zaune a kan cinyoyin uyayensu aka hefa su a cikin wuta haka kawai.
GwamnanMasari ya tabbatar wa mahalarta taron cewa koda Dabbobin sa ke cikin daji ba za su yi irin abin da yan ta’addan suka yi a kauyen Tsauwa da Dankar ba.
Gwamnan ya kuma Dora alhakin a kan Malamai masu wa azin musulunci da ba su fadakar da irin wadancan mutane ba a kan ka’idoji da tanaje tanajen musulunci a kan harkokin duniya da ilimi baki daya.
“Aikin Malamai ne masu wa azi su rika fadakarwa a dukkan inda aka je taron suna ko dun wani taron jama’a a kan irin koyarwar addinin Islama”.
Tun da farko sarkin katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya gargadi malamai masu amfani da hudubar Juma’a suna jifan ya uwansu malamai da kalaman batanci da haifar da rudani a cikin al’umma.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.