Home / Labarai / Jama’a Sun Ya Ba Da Kokarin Shugaban Majalisar Dokokin Kaduna Yusuf Ibrahim Zailani

Jama’a Sun Ya Ba Da Kokarin Shugaban Majalisar Dokokin Kaduna Yusuf Ibrahim Zailani

Jama’a Sun Ya Ba Da Kokarin Shugaban Majalisar Dokokin Kaduna Yusuf Ibrahim Zailani
Daga Wakilinmu Akaradan Kaduna
Sakamakon irin Namijin kokarin da shugaban majalisar dokokin Jihar Kaduna honarabul Yusuf Ibrahim Zailani, yake yi a koda yaushe domin ganin al’amuran addini da sauran dukkan fannoni sun inganta harkokin kasa baki daya.
Alhaji Jafaru Sambo shugaban ma’aikatan Kakakin majalisa Yusuf Ibrahim Zailani ne ya yi wannan yabon a wata takardar sanarwar da ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a Kaduna.
Inda ya ce a matsayinsa na wanda ya san irin yadda al’amura suke tafiya hakika mutanen Jihar Kaduna na bukatar Namijin kokarin shugaban majalisar.
Ya ci gaba da cewa Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani Garkuwan Musabakar Alkur’ani, jama’a na bukatar irin kwarewa da salon tafiyar da shugabanci irin nasa kasancewarsa mai matukar Sani da kwarewa a harkokin siyasa, musamman a yadda yake tafiyar da jagorancin majalisa a shekara daya da ta gabata.
Takardar da Jafar Sambo ya sanyawa hannu ta bayyana cewa kungiyar mataimaka na musamman da aka rabawa manema labarai.
‘’ Tun lokacin da aka Rantsar da shi a matsayin shugaban majalisa a ranar 25 ga watan Fabrairu 2020, ya jagoranci samar da kudirori 19 da suka zama doka da ke da amfani wajen ci gaban tattalin arzikin Jihar Kaduna baki daya”.
Yayan kungiyar sun fito fili sun bayyana farin cikinsu irin yadda shugaban majalisar ya jagoranci samar da kungiyar shugabannin majalisun dokokin Jihohin arewacin Nijeriya.
Wanda hakan zai ba su damar su zama wuri daya tare domin cimma aiwatar da ya dace jama’a su amfana, kuma an zabe shi a matsayin shugaban wannan kungiyar na farko.
Hon. Zailani ya kasance ya na da hannu a wajen ci gaban da Jihar Kaduna ta samu da dama karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ta fuskar samar da dokokin da za su taimakawa samun nasarar.
“Shi ne na farko wanda ya kirkiro gabatar da kasafin kudi da harshen Hausa domin jama’a Maza da Mata na can kasa su amfana sun San me ake yi, wanda yin haka zai ba su damar sanin me ake nufi da kasafin kudi”.
Saboda irin kokarin shugaban majalisar dokokin Jihar Kaduna Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani, wajen ciyar da daukacin al’umma gaba yasa aka bashi Garkuwan Musabaka na masarautar Zazzau baki daya a Jihar Kaduna.
Hatta ma’aikatan majalisar dokokin Jihar kaduna sun amfana da kayan tallafi a lokuta daban daban a lokacin jagorancin Honarabul Yusuf  Ibrahim Zailani a shekara daya da ta gabata.
Wannan kungiya ta yi addu’ar samun hadin kai da samun natsuwa tare da fahimtar Juna tsakanin bangaren majalisa da masu zartaswa a Jihar Kaduna, musamman kamar yadda aka gani a lokacin jagorancin Honarabul Zailani, da wannan ne muke yi masa fatan ci gaba da samun taimako daga Allah madaukakin Sarki.

About andiya

Check Also

CCMMD Urges Unified Action to End Gender-Based Violence in Nigeria Amidst UN 16 Days of Activism with Hope and Action

As the world commence the celebration of International Day for the Elimination of Violence against …

Leave a Reply

Your email address will not be published.