Home / Ilimi / JAMI’A TA TABBATA A FUNTUWA – HONARABUL ABUBAKAR DANDUME

JAMI’A TA TABBATA A FUNTUWA – HONARABUL ABUBAKAR DANDUME

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Honarabul Abubakar Muhammad dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Funtuwa da Dandume ya bayar da tabbacin cewa batun da ake yi na jami’ar kimiyyar kiwon lafiya da Gwamnatin tarayya ta kirkira tabbas an kammala magana za ta zauna a Funtuwa don haka kowa ya Sanya ransa a cikin Inuwa tare da natsuwa a game da lamarin.

Honarabul Barista Abubakar ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa ta wayar Salula da wakilin mu, inda ya ce “hakika batun kawo jami’a sabuwa da Gwamnatin tarayya ta yi garin Funtuwa har ma an kammala batun kowa ya amince za a ajiye ta a Funtuwa wannan batu ya zama kusan ace tabbas”, inji Honarabul.
“Ko a jiya sai da aka yi wani zama da Gwamna da kuma dukkan masu ruwa da tsaki a yankin Funtuwa an kuma amince saboda dai- daito ayi matsugunin jami’ar a Funtuwa, don haka lamarin ya yi Armashi kwarai”.
Saboda haka muna kira ga daukacin al’umma kowa ya Sanya ransa a cikin Inuwa domin bukata za ta biya nufi a game da batun samar da jami’ar da ake fatar a samu a garin Funtuwa.
Kamar dai yadda wakilin mu ya zagaya a ciki da wajen Jihar Katsina ya ga jama’ar Jihar musamman na bangaren yankin Funtuwa da ke da kananan hukumomi Goma sha daya da ake kira Karaduwa ko yankin Funtuwa suna ta bayyana murna da farin cikinsu a game da wannan jami’a da za a yi.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.