Home / Big News / Jami’an Tsaro A Kaduna Sun Gano Makaman Bangaren Kachalla

Jami’an Tsaro A Kaduna Sun Gano Makaman Bangaren Kachalla

Jami’an Tsaro A Kaduna Sun Gano Makaman Bangaren Kachalla
Mustapha Imrana Abdullahi
Jami’an tsaron da ke aiki a karkashin Rundunar tsaro ta Thunder Strike sun tabbatarwa da Gwamnati cewa sun samu nasarar samun bindigogi hudu kirar AK47 da suka tabbatar da cewa na bangaren marigayi Nasiru Kachalla ne.
Kamar yadda rahoton ya bayyana cewa makaman an samu gano makaman ne tare da taimakon bayanan sirri daga wadansu mutanen kauye.
Bayanin hakan na cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida na Jhar kaduna Malam Samuel Aruwan.
Indai zaku iya tunawa Nasiru Kachalla an kashe shi ne a watan Disambar shekarar 2020, a lokacin da suka samu matsala tsakaninsu da wadansu gungun mutanen da suka sato shanu, Lamarin dai ya faru ne a kan iyakar dajin Kajuru da Chikun
Kachalla tare da gungun mutanensa sun dade suna aikata laifuka da dama da suka shafi ta’addanci da suka hada da satar muhimman mutane da ta’addanci a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma yankin Chikun da Kajuru.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El- Rufa’I ya bayyana godiyarsa da samun wannan rahoton bisa aikin gano wadannan malamai, inda ya shawarci jami’an tsaron da su hanzarta wajen gano karin wasu makaman.
Kamar yadda takardar ta bayyana cewa ana kokarin ganin an samo wadansu karin makaman.
Ga dai bindigun da aka samu nan kamar yadda zaku gansu a cikin  hoto.

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.