Home / Labarai / Jam’iyar PDP A Jahar Sakkwato Ta Yi Dacen Jagora

Jam’iyar PDP A Jahar Sakkwato Ta Yi Dacen Jagora

A yau 18 ga watan Ramadan Maigirma jagoran Jam’iyar PDP a jahar Sokoto,  Sanata Aminu Waziri Tambuwal Mutawallen Sokoto,  zai jagoranci buda baki a gidansa dake Kontagora Road a cikin garin Sokoto, inda a kalla aka gayyaci sama da mutum 1000.
Haka ma Maigirma sanata zai raba kayayki ga magoyan Jam’iyar PDP mai albarka da suka kunshi buhuwan Shinkafa da kuma zunzurutun kudi ga magoya bayan jam’iyar PDP na mazabu 244 dake cikin kananan hukumomin jahar Sokoto 23.
Ga tsarin wadanda zasu amfana da wannan tallafin kamar jaka.
1. Dattawan jam’iyar PDP
2. Shugabanin jam’iyar PDP matakin jaha.
3. Shugabanin jam’iyar PDP matakin kananan hukumomi 23
4  Shugabanin jam’iyar PDP matakin mazabu 244 dake cikin kananan hukumomi 23
5.Dattawan jam’iyar PDP a kananan hukumomi 23
6. Mata magoya bayan jam’iyar PDP a kananan hukumomi 23
7. Matasa magoya bayan jam’iyar PDP a kananan hukumomi 23
8. Tsoffin kwamishinoni wadanda ke cikin jam’iyar PDP
9. Tsoffin masu ba gwanna shawara wadanda ke cikin jam’iyar PDP
10. Tsoffin mayan sakatarori da mayan daraktoci dake cikin jam’iyar PDP
11. Tsoffin Shugabanin kananan hukumomi 23 wadanda ke cikin jam’iyar PDP
12. Tsoffin ‘yanmajalisar jaha da na tarayya wadanda ke cikin jam’iyar PDP
13. Tsoffin kansiloli wadanda ke cikin jam’iyar PDP
14. Tsoffin ‘yantakarar majalisar jaha da na tarayya wadanda ke cikin jam’iyar PDP
15. Membobin kungiyar social media ta jam’iyar PDP.
16.Makada mawaka da maroka wadanda ke cikin jam’iyar PDP
Haka ma, baya ga wannan tanadi da ya game fadin jahar Sokoto,  Maigirma Sanata yayi wani tanadi na  musamman ga kananan hukumomi 7 da yake wakiltar a majalisar dattawa.
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Allah ya taimaki wannan jagora namu.
Allah ya kara karfafa jam’iyar PDP a jahar Sokoto da kasa baki daya.
Signed,
Hassan Sahabi Sanyinnawal,
Sakataren watsa labarai na PDP jahar Sokoto

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.