Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
An bayyana jam’iyyar APC a matsayin jam’iyyar da ke cikin hadari don haka lamari ne da ke matukar bukatar daukar matakan gaggawa.
Tsohon shugaban karamar hukumar Kalgo a Jihar Kebibi honarabul Umar Namashaya Digi, ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da kafar Talbijin ta Farin Wata.
Umar Namashaya Digi ya ce lamari ne da ke matukar bukatar a dauki matakan gaggawa wajen magance matsalar da APC ke ciki, musamman ganin samun jam’iyyar APC na da gwamnati ya fi kyau ace ba Gwamnatin APC.
Namashaya, ya kuma yi kiran cewa game da rade radin da ake yi ma cewa ana wani shirin Gwamna da Sanata a zabe mai zuwa za su fito daga karamar hukuma guda, wanda babu irin wannan a cikin tsarin Dimokuradiyya.
“Babu dole fa a cikin siyasa sai dai abi tsari irin na Dimokuradiyya, saboda idan aka ce dole to an kaucewa tsarin Dimokuradiyya”, inji Umar Namashaya Digi.
Ya kuma yi kira ga Gwamnan Jihar Kebbi ya fito domin yi wa jama’a cikakken bayani game da batarnakar da ake ganin na neman tarnake APC a Jihar Kebbi.
“Muna kira ga Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, Ministan Shari’a Malami duk su fito domin yi wa jama’a bayani gamsashshe.
Umar Namashaya ya kuma yi gargadi a kan yin dauki Dora a tsarin shugabanci wanda yin hakan bai cancanta ba