Home / KUNGIYOYI / Kungiyar Miyatti Allah Ta Nemi Gafara Ga Masari

Kungiyar Miyatti Allah Ta Nemi Gafara Ga Masari

Mustapha Imrana Abdullahi

 

Bayanan da ke shigo mana daga cikin garin Katsina na cewa kungiyar al’ummar Fulani ta Miyatti Allah Kautar hore ta nemi Gafarar Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da ya yafe mata a kan wadansu kalaman da aka ce Sakataren ta na kasa ya yi da suka bayyana karara cewa cin mutunci ne ga Gwamnan.

 

Reshen kungiyar na Jihar Katsina ya bayyana wa manema labarai cewa sun bi sahun babbar sakatariyarsu ta kasa inda suke nesanta kansu daga kalaman da ka ce sakataren kungiyar na kasa Saleh Alhassan, ya yi,inda ya yi wadansu kalamai marasa dadi ga Gwamna Masari.

 

 Sale ya dai nuna fushi da bacin ransa ga irin kalaman da ya ce Masari ya yi na cewa mafi akasarin masu satar jama’a a yankin arewacin Najeriya ana karbar kudin fansa al’ummar Fulani ne.

 

Shugaban kungiyar na Jihar Katsina, Hassan Kuraye, ya bayyana wannan nesanta kansu da wadancan kalamai a wajen wani taron manema labarai a Katsina. Inda ya roki Gwamnan gafara da ya gafarce su game da wannan lamarin.

 

 Wannan matsaya ta shugaban kungiyar reshen Jihar Katsina na zuwa ne a kasa da awayi 48 bayan Gwamna Masari ya yi magana da kafar yada labarai ta ait. Ya na mayar da martani game da kalaman sakataren kungiyar Miyatti Allah Kautar hore ta kasa, inda ya ce zai dauki mataki doka.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Izma Yamadi, wanda shi ne ya yi magana da manema labarai a madadin shugaban kungiyar na Jihar Katsina, Hassan Kuraye ya ce duba da irin muhimmiyar rawar da Gwamnan ya taka wajen dai- daita tsakanin Manoma da Makiyaya a Jihar, hakika irin wadannan kalamai sam ba su dace ba ko kadan.

Kalaman sakataren kungiyar na kasa ba su ne matsaya ko da yawun sakatariyar kungiyar ta kasa ba, shi yasa reshen kungiyar na Jihar Katsina suke nesanta kansu daga wadannan kalamai, inda suke jaddada idanunsu kan cewa sakatariyar kungiyar ta kasa na yin da na sanin wadancan kalamai nasa a yanzu.

Kungiyar ta ce nan ba da dadewa ba shugaban kungiyar na kasa tare da sauran mukarrabansa za su zo Katsina domin ziyartar Gwamnan, su kuma roke shi gafara game da lamarin.

Sun kuma bayyana aniyarsu wajen ci gaba da taimakawa Gwamnatin Jihar wajen kokarin da take yi na magance matsalar sace- sacen jama’a domin karbar kudin fansa da sauran ayyukan laifuka da wasu ke aikatawa.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.