Home / Labarai / Jam’iyyar PDP Ta Taya Tsohon Gwamna Makarfi Murnar Ranar Haihuwarsa

Jam’iyyar PDP Ta Taya Tsohon Gwamna Makarfi Murnar Ranar Haihuwarsa

…Sun Ce Shugaba Ne Abin Koyi,Mai Kokarin Hada Kan Al’umma
Jam’iyyar PDP ta kasa ta taya tsohon shugabansu kuma wanda ya yi Gwamnan jihar kaduna har karo biyu, Sanata Ahmad Muhammad Makarfi, murnar ranar haihuwarsa  da ya cika shekaru 66 a duniya.
Sanata Makarfi dai kwararren ma’aikaci ne da ya kare a fannoni daban daban, kuma kwararre ne a fagen gudanar da mulki,ga shi kuma kwararren masani a wajen aikin majalisa,da ke yin aikinsa tare da nuna jin kai da duk wani tausayin dan Adam, da ke kokarin hada kan yan kasa domin a samu ci gaban da kowa ke bukata.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke Honrabul Debo Ologunagba babban Sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar PDP na kasa.
A tsawon shekarun da suka gabata, Sanata Makarfi, ya dade ya na yin amfani da kwarewarsa ya na kokarin horar da jama’a, yin nuni ta hanyar da’a ladabi da biyayya matsayinsa na kwararren ma’aikacin Banki, kuma Malamin jami’a, kwararre a fannin gudanar da harkokin shugabancin jama’a da ya samu nasara a shugabanci irin na siyasa.
A lokacin da yake Gwamnan Jihar Kaduna ya nuna cikakkiyar kwarewar da ta bashi damar samun nasarori da dama a fannoni da yawa da suka inganta rayuwar al’umma a duk fadin Jihar Kaduna baki daya. A sakamakon irin zurfin kwarewarsa a gudanar da mulki, jihar Kaduna Kaduna amfana da samun zaman lafiya tsakanin al’umma da suka amfana da tsare tsare da kuma tanaje tanajen jam’iyyar PDP.
A majalisar Dattawa, ya yi amfani da kwarewarsa a matsayin shugaban kwamitin kudi wajen nuna yadda ake tafiyar da tsarin gaskiya da adalci, wanda sakamakon hakan kasa baki daya ta samu nasara.
Jam’iyyar PDP na farin cikin samun irin wannan kwarzon shugaba kamar Sanata Ahmad Muhammad Makarfi, a matsayin shugaban jam’iyya na kasa da ya ceto jam’iyyar a lokacin da aka shiga cikin wani halin jarabawa a fannin shugabancinta a kasa da kuma fuskar al’ummar kasashen waje.
Hakika jam’iyyar mu ta jinjinawa Sanata Ahmad Makrfi, saboda irin kokarinsa tare da sauran shugabanni da suka dage wajen sake Farfado da jam’iyyar da kuma ceto kasar daga hannun mulkin mallaka irin na APC.
Jam’iyyar PDP na taya wannan dan Najeriya mai kishin jama’a, murnar ranar haihuwarsa tare da yi masa addu’a samun lafiya da tsawon kwanaki masu amfani domin amfanin kasa da al’ummarta baki daya

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.