Home / Labarai / Karamar Hukumar Kajuru ba a kudancin Kaduna take ba – Miyetti Allah

Karamar Hukumar Kajuru ba a kudancin Kaduna take ba – Miyetti Allah

Musa Sunusi Abdullahi

Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah na kasa reshen kudancin Kaduna Alhaji Abdulhamid Musa Albarka ya ce akwai bukatar sake duba lamarin da ake nufi da kudancin Kaduna ganin yadda wasu ke yawan ambaton an yi rikici a kudancin Kaduna a duk lokacin da wani abu ya faru a yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Alhaji Abdulhamid ya ce babban abin takaici ne a duk lokacin da aka wayi gari ya ga wata kungiya ta fitar da takardar manema labarai tana ambaton kai hari a kudancin Kaduna idan an kai hari a karamar hukumar Kajuru ko Birnin Gwari ko Chikun, wanda a hukumance an san suna yankin Kaduna ta tsakiya ne.

“Kuma babban abin takaicin sai ka ga hatta ‘yan jaridu a jihar Kaduna da na kudancin Najeriya sun dauka suna yayatawa cewa an kai hari a Kudancin Kaduna alhali in za ayi magana a hukumance, ba a qabilance ko don wata manufa ta siyasa ba, karamar hukumar Kajuru tana karkashin sanatan Kaduna ta tsakiya ne ba sanatan Kudancin Kaduna ba. A matsayina na shugaban kungiyar Fulani makiyaya na kudancin Kaduna Kajuru ba ta a cikin yankina, haka abin yake a lokacin zabe na siyasa domin ‘yan Kajuru na zaben sanatan Kaduna ta tsakiya ce ba na kudancin Kaduna ba. Me yasa idan ana zaman lafiya ko idan an zo batun shugabanci da dimokradiyya ake sa Kajuru a Kaduna ta tsakiya amma da an samu rikici a yankin sai a sa ta a kudancin Kaduna?” Inji shi

Ya ce ya kamata masu yada irin wannan su fito su fadawa duniya da wane ma’auni suke yin lissafin wuraren da a hukumance suna wani yanki ne, amma su kadai su ke kokarin canza su zuwa wani yanki na daban. “Shin da ma’aunin kabilanci ne ko na addini ko bisa wane dalili ne na siyasa?” Ya yi tambaya.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.