Home / Kasuwanci / KASUPDA Da Yan Kasuwar Bacci Sun Tattauna Har An Fara Tushe Kasuwar

KASUPDA Da Yan Kasuwar Bacci Sun Tattauna Har An Fara Tushe Kasuwar

Daga Imrana Abdullahi
Tun bayan tattaunawar da aka yi tsakanin hukumar kula da tarin gine gine ta Jihar kaduna da kuma shugabannin yan kasuwar Bacci da ke garin Kaduna arewacin tarayyar Nijeriya tuni har hukumar ta fara aiwatar da aikinta domin samun damar yin gini na zamani a kasuwar.
Rahotannin da muke samu na bayanin cewa tuni aka cimma matsaya bayan tattaunawa tsakanin hukumar kula da Gine gine a Jihar Kaduna KASUPDA da kuma shugabannin kasuwar Bacci kaduna.
Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa an tattauna ne tsakanin juna a ofishin hukumar KASUPDA inda kuma aka samu fahimtar Juna nan take.
Kamar yadda majiyar ta shaida mana cewa an tattauna sosai kuma an nuna masu cewa ABU ne fa na ci gaba da yazo, kuma ba kasuwar Bacci kawai bane akwai kasuwanni irin su Sabon Garin Zariya, kasuwar Dan Magaji Zariya da kasuwar Kawo sai kuma ita kasuwar Baccin kanta da aka tattauna da shugabannin kungiyar kasuwa
Majiyar ta shaida mana tuni aka samu fahimtar juna kuma sun ga ya dace ne kawai su amince da ci gaban da za a samu
Wakilinmu dai ya ziyarci kasuwar kuma yaga irin yadda yan kasuwar ke cire kayansu domin ba Gwamnati damar ta gudanar da aikinta a wurin.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.