Home / News / KATIN ZABE NA DA MATUKAR MUHIMMANCI A LOKACIN DA MUKE CIKI – NASIR DAURA

KATIN ZABE NA DA MATUKAR MUHIMMANCI A LOKACIN DA MUKE CIKI – NASIR DAURA

IMRANA ABDULLAHI

An bayyana karin zabe a matsayin wani abu mai matukar muhimmanci da ke zaman wani Makamin da kowa zai yi alfahari da shi wajen zabar abin da kowa ke bukata a kowa ne irin mataki.

Dan majalisar dokokin Jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Daura Nasir Yahya Daura ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin Daura.

“Saboda wannan katin zaben ne yan majalisa ke cewa shi ne makaminka a ranar zabe domin zaka yi amfani da shi a ranar zabe domin zabar abin da kake bukata, somin haka ne muka ganin katin zaben nan keda matukar muhimmanci fiye da komai a irin yanayin da muke ciki a yanzu saboda haka ya zama wajibi al’umma musamman a wannan yankunan na mu da su fito ga dukkan wadanda suka kai adadin shekaru Goma Sha Takwas da wanda na su ba su yi ba a can baya da wadanda keda bukatar yin gyara a nasu da kuma duk wanda nasa katin ya bace a tabbatar da cewa an fito an yi wannan katin zabe domin da shi ne za a yi amfani a tabbatar da an samu abin da ake so a zaben shekarar 2023 da zai taimaki al’umma kuma ya kawo wa kasar ci gaba bisa yadda muke gani idan Allah ya kaimu”, in ji dan majalisa Nasir.

Dan majalisa mai wakiltar Daura ya ce ya na kira ga al’ummar kasa baki daya da a ci gaba da addu’ar neman zaman lafiya a kuma hada kai a tabbatar da cewa an yi abin da ya dace ayi wajen ganin an taimaki Najeriya domin ita ce ke a cikin zukatan mu, yankunan mu kuma mu yi kokarin ganin min taimaka domin mu yi abin da zamu yi na kirki domin a Dora yankunan a kan dai- dai domin ganin al’umma sun yawaita da jin dadi da walwala saboda zaben da muke fuskanta za mu yi shi a cikin lumana, jam’iyyar APC da nake cikinta ita keda nasara kuma za ta samu nasara da yardar Ubangiji.

Ya ci gaba da cewa ya na yi wa al’umma murnar babbar Sallah da fatan samun ci gaba da zaman lafiya da karuwar arziki.

“Kuma ina yi wa shugaba Muhammadu Buhari murnar samun karin nasara a cikin Mulkinsa ya aiwatar da aikin Dora Najeriya a kan turbar ci gaba da yake kokarin Dora kasar a kai ya cimma burinsa ya Dora najeriya a kan dai- dai, bukata da biya nufi”, inji Nasir.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.