Home / Labarai / Sakon Murnar Babba Sallah Ga Al’ummar Musulmi Daga Dokta Iyorchia Ayu, Shugaban Jam’iyyar PDP Na Kasa

Sakon Murnar Babba Sallah Ga Al’ummar Musulmi Daga Dokta Iyorchia Ayu, Shugaban Jam’iyyar PDP Na Kasa

 

(Imanin Mu Ya Fi Karfin Abin Da Muke Jin Tsoro)

 

 

Ya yan uwana al’ummar Musulmi tare da murna da farin ciki nake taya daukacin al’umma Musulmin Najeriya da kuma Duniya baki daya murnar babbar Sallah

Hakika babban alfanun da ke cikin sadaukarwar yin layya, alwai nuna kauna, biyayya da Soyayya kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya aikata a cikin Al’ kur’ani mai girma saboda haka nake bayar da shawara ga al’ummar Musulmi da kada su yi sakaci da irin wannan koyarwar a lokacin da suke murna da kuma su yi addu’o’i ga kasar mu Najeriya.

Abubuwa da dama ba a dai- dai suke ga jama’a da kasar ba don haka ya dace a tabbatar da mayar da dukkan lamari ga Allah saboda Imanin mu ya fi karfin abin da muke jin wa tsoro a garemu.

Najeriya ba ta taba tsintar kanta a cikin irin wadanan matsalolin ba da lamuran suka tabarbare. Amma kada mu bari tsoro ya danne (ya kashe) farin cikin mu. Mu yan Najeriya ne. Don haka ba zamu yi saurin karaya ba. Muna da imanin cewa abubuwa za su gyaru nan gaba kadan.

Saboda haka ne muke kokari a koda yaushe domin komai ya inganta. Muna nuna jimamin yan uwan mu da suka mutu. Mun binne wadanda muke kauna. Muna kuma yin taka tsan- tsan a duk lokacin da muke tafiye tafiye. Muna yin aron kudi domin biyan kudin fansa ga masu satar mutane. Amma duk da haka kuma muna nuna farin ciki a lokacin yin haka. Don haka tsammanin alkairin da muke da shi ya fi karfin damuwarmu; don haka wannan kwarin gwiwa ne da muke da shi da zai zamar mana alkairi nan gaba.

Mun ki barin matsalar tattalin arzikin da muke ciki ya hana mu yin bikin murna da shagulgula. Za mu iya kasance wa ba mu da kudin da za mu sayi dabbobi mu yanka da kuma samun sauran kayan jin dadin rayuwa, Duk da haka muna yin bikin murna. Saboda imanin mu da Allah ba zai ta ba girgizawa ba ko kadan.

Don haka nake dokin yin tuni a gare ku cewa wannan hutun Sallar Sallar za mu yi a karkashin wani mawuyacin yanayi. Sun yanke mu, Amma duk da haka muna yanka Ragunan mu a cikin zaman lafiya tare da tunanin cewa nan gaba kadan al’amura za su inganta sosai.

Da wannan ne nake taya yan Najeriya da al’ummar Musulmi, mussaman abokainmu da sauran yan uwa murnar bukukuwan Sallah lami lafiya.

Dokta Iyorchia Ayu
Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.