Home / Labarai / Kotu Ta Iza Keyar Abduljabbar Zuwa Gidan Yari

Kotu Ta Iza Keyar Abduljabbar Zuwa Gidan Yari

Mustapha Imrana Abdullahi
Kotu a Jihar Kano ta caji Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara, da laifin yin batanci, tunzura jama’a sakamakon hakan ta mika ajiyarsa gidan gyaran hali, wato kurkukun da ke Kano.
Indai Za’a iya tunawa Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara, Malamin addinin musulunci ne da ke Kano wanda ya rika yin kalaman tare da yin sharhin addinin Islama da suka rika haifar da rudani a tsakanin musulmi game da Annabi Muhammadu (S.A.W) wanda sakamakon hakan kotu ta caje shi da laifin yin batanci.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da da hannun Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Malam Muhammad Garba, da ke nuni da cewa faruwar hakan ya samo asali ne bayan samun rahoton yan Sanda na farko daga ofishin babban mai shari’a kuma kwamishinan ma’aikatar shari’a bayan hakan aka shirya gurfanar da Malamin gaban kuliya.
An dai gabatar da Abduljabbar ne a gaban alkalin babbar kotun shari’ar musulunci da ke Kofar Kudu, da Alkali Ibrahim Sarki Yola, w ranar Juma’a 16 ha watan Yuli inda aka tuhumi malamin da laifukan yin batanci, da kuma kokarin tunzura jama’a da duk aka ambaci laifukan baki daya a gaban kotu.
Takardar ta kara da cewa bayan zaman kotun, an dage sauraren karar zuwa ranar 28 ga watan Yuli, shi kuma Malamin ya ci gaba da zama a wurin Yan Sanda har zuwa ranar Litinin, lokacin da aka iza shi gidan gyaran hali har zuwa ranar.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.