Home / Labarai / KU KUJEWA MIYAGUN ABOKAI, JITA – JITA DA GUTSIRI TSOMA – KAILANI MUHAMMAD

KU KUJEWA MIYAGUN ABOKAI, JITA – JITA DA GUTSIRI TSOMA – KAILANI MUHAMMAD

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Wani uban Anguna guda Uku da ya Daura masu aure a yau Juma’a Iniiniya Dokta Kailani Muhammad ya bayyana cewa batun aure a matsayin Ibadar Allah tare da yin kira ga ma’auratan da su gujewa yan gutsiri tsoma, gulma da duk nau’in Jita – jita.
Injiniya Kailani Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala daurin auren da aka yi a garin Kaduna.
An dai Daura auren ne a masallacin Shaikh Khamis Al-Misri, da ke cikin garin Kaduna bayan kammala Sallar Juma’a.
Kailani Muhammad ya kuma yi kira ga Amare da Angunan  baki daya da su gujewa masu gulmace gulmace da ka iya kawo masu maganganu irin na gutsiri tsoma, bisa la’akari da yadda ake samun matsalolin aure sakamakon kananan maganganu a cikin al’umma.
Sai ya yi addu’ar Allah ya bada yadda za a yi cikin zaman lafiya da lumana.
“Ayi kokarin rike ciki ta hanyar samun ingantacciyar ciyarwa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar”.
An Daura auren Abdullahi, Sadiq da Abdurrahman wadanda duk yayan Injiniya Dokta Kailani Muhammad ne da ya aurar da su baki daya.
Al’umma da dama ne daga ciki da wajen Najeriya suka halarci taron Daurin auren da kuma gagarumar walimar cin abinci da aka yi a gidansa a unguwar Rigasa Kaduna.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.