Home / Labarai / Masari : Ayi Koyi da Kungiyar Ma’aikatan Lafiya wajan Samar da Motocin Sufuri

Masari : Ayi Koyi da Kungiyar Ma’aikatan Lafiya wajan Samar da Motocin Sufuri

 

Daga Hussaini Yero, Funtua

 

 

Gwamna Aminu Bello Masari , da ya samu wakilcin mai bashi Shawara bangaren Ma’aikata Hon Tanimu Lawal Saulawa , yayi Kira ga Kungiyoyin Ma’aikatan Jihar Katsina da suyi koyi da Kungiyar Ma’aikatan Lafiya wajan Samar wa Mambobin Motocin Sufuri dan dogara da kan su.

 

 

Gwamna Masari yayi Wannan kiran ne ajiya Alhamis Wajan bikin Kaddamar da Motocin Sufuri kirar Gof ,guda biyar a Ofishin Kungiyar da ke Katsina.

 

 

Masari ya jinjina wa Kungiyar Ma’aikatan Lafiya wace a duk Shekara sai ta samar da wani abunda Mambobin kungiyar zasu amfana da shi na samun kudin shiga . Wannan ya tabbatar da cewa,lallai lafiyar rayuwar su suke san ingantawa da dan abunda suke samu na dauni daga Ma’aikatan su.inji Gwamna Masari.

 

 

” Akan haka ne yayi kira da babbar mirya ga sauran Kungiyoyin da suyi koyi da wadanda Kungiyar dan samun cigaban Mambobin.

Anasa jawabin Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Lafiya na Kasa , Kwamaret da ya samu wakilcin ,Ma’taimakinsa Kwamaret Kabiru Ado Minjibir ,ya bayyana cewa,Wannan Kungiyar ta zamo kazaran gwajin Dafi wajan kawo cigaban Manbobin kungiyar wajan samun hanyoyin kudin shiga dan a shekarun baya sun Kaddamar da gidan Masaukin Baki da Wajan saida Abinci Kuma gashi yanzu sun Samar da Motocin Sufuri dan karin samun kudin shiga dan jindadin Mambobin kungiyar.wannan kokarin shubanin Kungiyar bamu san abunda zamu musaltashi da suba.inji Kwamaret Mijibir.

 

 

Ansa Jawabin Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Lafiya na Jihar Katsina , Kwamaret Manir Sule Funtua ya bayyana cewa,sun samu nasara samar da abubuwan samar da kudin shiga ne ta hanyar dauni da ake cirewa ko wane Ma’aikacin Lafiya ,da sune suka taro suka Samar da Masaukin Baki da Shaguna da Wajan saida Abinci ,yau Kuma gashi munsamar da Motocin Sufuri dan Kara bunkasa hanyoyin kudin shiga dan biyan bukatun Ma’aikatan mu da jindadin su.ta kowane sashe.inji Kwamaret Manir Sule Funtua.

 

 

“Kwamaret Manir Sule ya Kara da cewa, Kungiyar Ma’aikatan Lafiya na bada Tallafin Kudade ga masu Karatu da Abinci ga Marayu.da magunguna da sauran su.

Da ya koma akan ayyukan cigaban Kungiyar Kwamaret Manir ya bayyana cewa , yanzu haka munsamar da Gidan Masaukin Baki da Shaguna Mai suna Kwamaret Hussaini Hamisu.kuma munsamar da Filin 40 na gini hadin gyuwa da Kungiyar NLC .Kuma yanzu haka muna Gina gidaje Dari biyu a Kananan hukumomin Mulunfashi da Funtua.da dai sauran ayyukan cigaban da Kungiyar keyi dan cigaban Ma’aikatan Lafiya da ke cikin Jihar Katsina baki daya.

 

A karshe yayi godiya ga Gwamnatin Jihar Katsina, Karkashin jagorancin Gwamna Bello Masari wajan Basu hakokin su.da kuma magance duk wata matsala da ta taso na Ma’aikatan su na Lafiya.

About andiya

Check Also

NTI in Collaboration with UNESCO TRAINS 250 Teachers on HIV Education, Family Life

By; Imrana Abdullahi The Director and Chief Executive of NTI, Prof. Musa Garba Maitafsir said …

Leave a Reply

Your email address will not be published.