….Alhaji Musa Yakubu A Lokacin Da Yake Gabatar Da Jawabinsa
Daga Wakilin mu a Kaduna
Shugaban kamfanin zuba jari da harkar gidaje Alhaji Musa Yakubu ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da kulab din kwallonsa ya samu a lokacin bude gasar wasan kofin da kungiyar dilolin mota suka Sanya domin zaman lafiya ” Car Dealers Peace and Unity Soccer Competition” da aka buga a filin wasa na tunawa da Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Kaduna da Yammacin ranar Asabar.
Hakika na ji dadi da nasarar da aka yi, haka kuma da sauran yan wasan da suka yi wasan domin kowa ya bayar da gudunmawarsa Gwargwadon iko har nasara ta tabbatar.
Da yake ganawa da manema jim kadan bayan kammala gasar da kulab din Musaco Motors ya samu nasarar lashe kulab din Urgent Motors da ci 3 – 1wanda hakan ya ba su nasarar zama Zakaru a rukuni na B na masu halartar gasar, ya ce za su kara kwazo a gasar nan gaba.
“Muna murna da wannan nasarar da muka samu duk da tun farko ba mu shirya ba domin mun yi rajistar shiga gasar a makare”, inji shi.
Alhaji Yakubu ya ce koda kulab dinsa bai samu nasara ba za su karbi dukkan abin da Allah ya yi da kyakkyawar manufa su kuma taya duk wadanda suka samu nasara murnar samun ta domin manufar da aka Sanya a gaba duk daya ce, ta a samu cikakken hadin kai tsakanin masu harkar sana’ar sayar da motoci a Jiha baki daya”.
Da aka yi masa tambaya a kan ko yaya masu kula da gasar wato alkalan wasa suka gudanar da aikinsu sai ya ce sun yi komai bisa gaskiya da adalci.
Shugaban kamfanin na Musaco wanda kuma ya kasance shi mai yin gasar harkar tseren motoci ne kuma har ya samu nasarar lashe kyaututtuka da dama, ya jinjinawa wadanda suka shirya gasar, abin da ya bayyana da cewa babu abin da za a hada da shi wajen kokarin kawo hadin kai tsakanin masu sana’ar mota.