Daga Imrana Abdullahi
Honarabul Sani Rabi’u Bako, shugaban kungiyar ci gaban al’ummar cikin garin Kaduna ne mai suna KADDA ya bayyana nasarorin da kungiyar ke samu da cewa wani al’amari ne daga Allah madaukakin Sarki.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya tattauna da manema labarai a cikin garin Kaduna jim kadan bayan kammala taron kungiyar na shekara shekara inda aka gabatar da muhimman jawabai da kuma bayar da satifiket da lambobin karramawa na shekarar 2023.
Sani Rabi’u Bako, ya ci gaba da cewa duk da wannan kungiyar ba ta siyasa ko samun kudi ba ce, amma dai ta na gabatar da muhimman ayyuka a bangarorin ciyar da al’umma gaba.
Da suka hada da taimakawa Marayu, koyawa yara sana’o’i, koyawa yara karatun dabarun yadda za su rubuta jarabawar NECO da WAEC da kuma JAMB da nufin samun manyan gobe masu ilimi da hazaka.
Kuma kungiyar na gabatar da aiki a kan samar da Zakka da rabawa mutanen da suka cancanci a ba su da suke a cikin jama’a.
“Na kungiya ba ce ta cin riba ba sai dai kawai ana yin ayyukan ne domin a taimakawa jama’ar yankin mazabun Doka, Shaba, Gaji da Mazabar Liman duk a cikin yankin karamar hukumar Kaduan ta Arewa
“Muna kuma taimakawa Mata masu bukatar taimako da marayu ta hanyar sana’o’i da sauransu da masu fitar da zakka a rabawa al’umma da ba su da hali.Muna kuma bi domin tabbatar da cewa akwai zaman lafiya a wannan yankin, kadan kenan daga cikin irin aikace aikacen da kungiyar ke aiwatarwa
Muna kokarin yin aikin magance matsalar masu sara suka da kuma yan shara da masu Kwacen waya duk ana hada hannu tare da yan Sanda da kuma jami’an JTF a samar da tsaron lafiya da dukiyar jama’a, saboda haka muke yi wa Allah godiya a kan irin saukin da muka samu ba kamar jiya ba.
Honarabul Sani Rabi’u Bako ya kuma ce suna ta yin shirye shirye domin ganin me za su yi a shekara mai zuwa ta 2024.
” Mun taimakawa marayu sama da dari biyu da kuma wadansu mutane sama da dari biyar da kuma biyawa yara kudin makaranta na NECO, WAEC da jarabawar JAMB, kuma akwai yan siyasar mu da ke taimakawa da sauran al’umma duk a hakan ne ake taimakawa, wannan ne a takaice abin da ya kawo mu a wurin taron mu da aka tara jama’a aka gaya masu abin da kungiyar KADDA ke aiwatarwa.
Da yake gabatar da mukala a wajen taron Farfesa Kabiru Isa daga jami’ar Ahmadu Bello Zariya Dogon jawabi ya yi a kan muhimmancin ilimi da kuma irin yadda ake samu ci gaba a wajen tafiyar da al’amuran duniya musamman ta hanyar yin amfani da yanar Gizo.
Farfesa Kabiru ya yi kira ga daukacin al’umma da su hanzarta rungumar hanyoyin samun ci gaba na zamani domin gudun kada a bar su a baya.
Da yake gabatar da mukala mai taken gudunmawar matasa wajen ci gaban al’umma Dokta Aliyu Adamu Isa bayyana matasa ya yi da cewa mutane ne masu matukar muhimmanci a cikin al’umma.
Matasa za su iya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban kasa da al’umma baki daya
Kuma ya dace matashi ya zama mai dogaro da kansa a koda yaushe, ya kuma rika yin aiki da kula ta hanyar tabbatar da yan’uwantaka tsakaninsa da Juna, matashi ya rika danne zuciya a koda yaushe kafin gabatar da al’amura.
Sai dai ya dace a rika karfafa wa matasa domin ba su kwarin Gwiwa saboda matasa na saurin yin gangamin tara sauran matasa yan Uwansu a duk lokacin da wani abu ya faru.
A rika sauraren matasa a na shigo da su a cikin gudanar da harkoki a yau da kullum ta yadda za a rika Koyar da su a koda yaushe.
Sai an taimaka wajen hana matasa yin abin da bai dace ba da lokutan da suke da shi kasancewar matasa na da dimbin lokacin da suke aiwatar da wadansu ayyukan da bai dace ba
“Saboda a mafi yawan lokuta idan matashi ya ga karatu ko makaranta ba za su bashi abin da yake bukata ba sai ya koma ya nemi wani abun daban da yake ganin zai bashi abin da yake so, don haka sai an yi a hankali a koda yaushe.
Alhaji Abdul’Aziz Muhammad mai bayar da shawara a kan abin da ya shafi tsaro ga shugaban hukumar kula da yankin birnin Kaduna, Samuel Aruwan kamar yadda aka bani sako cewa hakika wannan hukumar za ta bayar da gudunmawar da ta dace domin samun ci gaban al’umma baki daya.
Alhaji Bala Muhammad Tijjani ya gabatar da jawabin Uban kasa ina cikin garin ciki a koda yaushe saboda wannan kungiya da ke zaman mataimakiya a gare ni
Ko a zamanin da can ayyukan kungiya irin wannan mataimakiya ce ga shugabanni tun a can baya.