Daga Mustapha Imrana Abdullahi
Bashir Sharif, Kwamandan Agaji ne na kungiyar Fityanul Islam daga Jihar Kaduna kuma mataimakin ma’aji na kasa baki daya ya jagoranci sauran mambobin kungiyar inda suka kai wa Farfesa Kailani Mihammad Ziyarar bam girma da taya murnar matsayin Farfesa da ya samu.
Kamar yadda suka bayyana wa manema labarai cewa ” sun zo ne domin yi wa Allah madaukakin Sarki godiya bisa daukakar da Farfesa Kailani Muhammad ya samu, saboda duk inda naku mai taimakon al’umma ya samu matsayi babban abin da zamu nuna mashi, shi ne farin ciki da kauna kuma ayi masa addu’ar neman kariya daga ubangiji madaukakin sarki ya kare shi ya kuma kare zuri’a baki daya. taimakon da yake yi wa al’umma ya ci gaba da ikon Allah”.
Da yake tofa albarkacinsa ga wadanda suka kawo ziyarar mai suna Dauda Abdulmumini cewa ya yi sun zo ne domin a taya Farfesa Kailani Muhammad murna da kuma yi masa addu’a
Muna yi wa Allah godiya da cew la duk abin da Farfesa Kailani Muhammad ke yi duk ya na yi domin Allah ne don haka baya son a dinga fadi saboda haka sai dai kawai ayi godiya kuma Allah ya kara daukaka shi
Haka suma mata cewa suka yi hakika Farfesa Kailani Muhammad na taimakawa mata ta hanyar ba su jari da kuma koya masu sana’o’i domin ko a kwanan nan ma sai aka bude wurin Koyar da sana’o’i ga shi nan har sun yi sati biyu ana koya masu sana’a.
“Gari gari duk mata sun Sani cewa ana taimaka masu daga Farfesa Kailani Muhamamd, kasancewarsa mutum mai yi domin Allah sai Allah ke kara daukaka shi a koda yaushe.
Ita ma Asabe Abubakar ba a barta a baya ba daukaka ta samu har Shaikh Dahiru Usman Bauci ya san abin da Kailani Muhammad ke yi wa jama’ar Jihar Kaduna da Najeriya baki daya hakan ne yasa aka turo jama’ar Fityanul Islam a kan su taya shi murnar arzikin matsayi na Farfeaa da ya samu.
“Ya Gaji alkairi don haka aikinsa ne ba wata tantama don haka muna yi wa Allah godiya sosai mara iyaka”.