Home / KUNGIYOYI / Kungiyar Gwamnonin Arewa Ta Yi Ta’aziyyar Shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Argungu

Kungiyar Gwamnonin Arewa Ta Yi Ta’aziyyar Shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Argungu

Daga Imrana Abdullahi

 

Shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin tarayyar Najeriya kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa cike suke da alhini da bakin ciki dangane da rasuwar fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Abubakar Giro Argungu wanda ya rasu jiya bayan gajeruwar rashin lafiya.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan (Hukumar Yada Labarai) na Gidan gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli ne ya gabatar da sanarwar a jiya, inda ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ba ga al’ummar musulmi kadai ba har ma da daukacin yankin Arewa da Najeriya baki daya.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce marigayi Sheikh Argungu fitaccen malami ne kuma shugaba abin koyi da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada Sunnar Annabi Muhammad (SAW).

“Rayuwar Sheik Abubakar Giro Argungu ta kasance misali mai haske na sadaukar da kai ga koyarwar Musulunci da inganta zaman lafiya tsakanin juna.  Gudunmawar da ya bayar wajen neman ilimin addinin Musulunci ya bar tarihi da ba zai gushe ba a cikin al’ummar Musulmin duniya baki daya da kuma a zukatan mutane da dama, kuma abin da ya gada zai ci gaba da zaburar da al’umma da kuma al’ummomi masu zuwa”.

Gwamnan a madadin gwamnati da al’ummar jihar Gombe ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin.

Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa ya kuma mika sakon ta’aziyyar sa ga shugabannin kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatissunnah JIBWIS inda Sheikh Abubakar Giro Argungu ya taka rawar gani wajen ciyar da addinin Musulunci gaba, tare da nuna rashin jin dadin rashinsa, amma kuma koyarwarsa za ta rayu a matsayin haske mai jagora”.

Gwamna Inuwa ya kuma jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kebbi da daukacin al’ummar Musulmin Nijeriya, inda ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma saka masa da mafificin Alkhairinsa a Jannatul Firdaus.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.