Home / KUNGIYOYI / KUNGIYAR KWADAGO RESHEN JIHAR KADUNA TA DAKATAR DA  YAJIN AIKI

KUNGIYAR KWADAGO RESHEN JIHAR KADUNA TA DAKATAR DA  YAJIN AIKI

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa karkashin jagorancin Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ta bayyana cewa a kokarin ta na ganin ta tabbatar da yin biyayya ga uwar kungiyar ta kasa da ta Dakatar da  batun yajin aiki da suka shirya gudanarwa a ranar Alhamis mai zuwa.
Ayuba Magaji Sulaiman ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da suka shirya a ofishin kungiyar kwadago ta “NLC” a Kaduna.
A wata takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar kwadago ta kasa Kwamared Ayuna Wabba da kuma sakatare Janar Kwamared Emmanuel Ugboaja duk an yi bayani filla filla game da batun yajin aikin da uwar kungiyar ta dakatar.
Kamar yadda suka yi bayani cewa sun dauki wannan matakin ne sakamakon irin yadda Gwamnatin tarayya ta dauki matakin Dakatar da batun yin karin farashin mai da kungiyar ta ce zai iya Jefa yan Najeriya cikin wata mummunar matsalar rayuwa.
Kamar yadda Kwqmared Ayuba Magaji Sulaiman ya tabbatar wa da duniya cewa “ba za su ta ba amince wa da irin yadda lamarin ake kokarin Jefa dimbin al’ummar kasa cikin mawuyacin hali ba, mu muna kokarin kare hakkin ma’aikata ne da sauran dimbin jama’ar kasa baki daya din haka a kullum za mu ci gaba da kokari a kan hakan”. Inji Ayuba.
An kuma rera wakar kungiyar kwadago domin karawa yayan kungiyar kaimin ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya ga kungiyar Kwadago.
Ayiba Magaji ya ci gaba da bayanin cewa kamar yadda kuka Sani muna da kungiyoyin da ke tare da kungiyar Kwadago har su 43, akwai kuma sauran wadansu kungiyoyin da ke tare da kungiyar Kwadago da suka hada da na masu rajin kare hakkin bil’adama.
“Da yan kungiyar mata yan kasuwa, masu sana’ar haya da Babura masu kafa uku da dai dimbin kungiyoyi da dama amma duk muna shaida masu cewa mun Dakatar da batun yajin aikin kamar yadda aka tattauna batun a matakin Gwamnatin tarayya”.
Yan kwadagon sun ce da zaran bangaren Gwamnati ya ci gaba da cewa zai kara farashin man to babu wani abin da za a yi sai dai kawai yayan kungiyar kwadagon su sake daukar mataki tun da daman dakatar wa aka yi.
Wadanda suka halarci taron manema labaran sun hada da yayan kungiyar, dalibai da sauran kungiyoyi kamar na kare hakkin dan adam da sauran yan Najeriya.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.