Home / News / Kwamishina Samuel Aruwan Ya Jinjinawa Wadansu Yan Kishin Kasa

Kwamishina Samuel Aruwan Ya Jinjinawa Wadansu Yan Kishin Kasa

Imrana Abdullahi daga cikin kaduna
Kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin cikin gida da tsaro na Jihar kaduna Samuel Aruwan a kan hanyarsa ta dawowa kaduna daga Jaji ya tsaya domin yin jinjina ga wadansu mutane yan kishin kasa da suka yi aikin tsaftace dajin da yan ta’adda ke labewa a wani bangare na dajin da ke kusa da unguwar Rigasa.
Su dai wadannan manoma sun kama wannan aikin ne domin ganin an samu cikakken sarari a wannan dajin.
Shi dai Samuel Aruwan ya tsaya ne domin yin godiya ga manoman da suke kusa da tashar Jirgin kasa da ke Rigasa da suke aikin gyaran wurin baki daya ta yadda za a hana batagari samun wurin labewa.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.