Daga Imrana Abdullahi
Kamar yadda tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya samu halartar babban taron manema labarai da Uwar jam’iyyar ta kira a Abuja inda suka koka a game da matsalar da ake samu tsakanin Hukumar Zabe ta kasa da jam’iyyar ADC da a jiya suka samu labarin fitar da sunayen shugabannin jam’iyyar karkashin jagorancin Sanata Devid Mark, abin da Kwankwaso ya ce ba za su amince da abin da hukumar zaben ta aiwatar ba Sam.
Kwankwaso ya ce, “ya na bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga abin da taron ya cimma na a shekarar 2027 m, dole ne a bar Yan Najeriya su zabi shugabanninsu ta hanyar yin amfani da jam’iyyu.hukumar zabe ba ta da ikon matsawa ta hanyar yin karfa karfar kaka ba wa jama’a wani dan takara, musamman idan aka yi la’akari da cewa Najeriya ce hamshakiyar kasa a Afirka da ke aiwatar da dimokuraɗiyyar.
– RMK
THESHIELD Garkuwa