Home / Labarai / LABARIN DAN KASA A TURAI – KASHI NA BIYU

LABARIN DAN KASA A TURAI – KASHI NA BIYU

 

INDA AKA TSAYA: Sai Dan Kasa ya daga hannunsa na dama, yace “HIGH 5”. Bature ya wangame baki da murmushi, ya daga nashi hannun ya mayar masa. Bature ya shiga mota yana murmushi, suka yi gaba. Dan Kasa na tsaye da sabuwar jaka, ga Ghana-Must-Go a gefensa. A ranshi yace “YAU GA DAN KASA A TURAI”.

CIGABA: Da me zai ji? Sabuwar jaka ko kallon dogayen gine-gine? Sai dubawa yake ko zai ga dan achaba amma shiru, ko babur daya bai gani ba. Wani kanshi da wajen yake yi, sai kace ana soya naman kaji, ga bishiyu kamar ana basu abinci. A ranshi yace “tashin hankali, ni ko a nan na samu wajen kwana, ai bani da matsala. Sai dai ina bukatar gidan sauro don na san saurayen Amurka zasu yi manyan hakora. Kalli jama’ar gari duk kowa a koshe. Ba kamar gida Najeriya ba.”

Dadi ya ishe shi, sai ya dubi sabuwar jakar shi. A ranshi yace “wannan jaka sai kace ta mango-pak?”. Sai ya koma gefe karkashin bishiya, ya zauna, ya fara budewa ya dudduba aljihunanta.

Nan take ya yanke shawarar mayar da kayansa dake cikin “GHANA-MUST-GO” zuwa cikin jakar. Bude wani dan karamin aljihu keda wuya, sai ga kudi cukus, daloli ‘yan dari-dari. Idanunshi suka bude. Duk da cewa yana rike da dala dari biyu a cikin aljihunsa da abokinsa Sani Ballack ya bashi aro, sai dai yawan wadannan daloli sun bashi tsoro.
Yayi maza ya waiga, ya gani ko turawa nan suna kan hanyar dawowa. Da ya ga babu kowa, sai ya fara dube-dube ya gani ko wani na kallonshi. Duk zuciyarsa sai bugawa take yi, jikinsa na rawa. A ranshi yace “Kai! Wannan shigo-shigo ba zurfi ne”. Sai ya rasa abunda zai yi. Ya bar jakar ne a nan wajen yayi ta kansa, ko ya jira ya gani in turawa zasu dawo? Gashi bai san ko nawa bane, kuma tsoron taba kudin yake. A nan ne ya tuna labaran Najeriya dake cewa wani lokacin mutum yakan taba kudin haram ya zama doya. Dan Kasa dake son cin doya, yana fargabar a ce yau shine za’a cinye. To ko wajen ‘yan sanda zai kai? Amma a ina suke? Sai ya tuna cewa a Amurka yawanci kiran ‘yan sanda ake ta wayar tarho. Amma ya ake kiran su, kuma gashi bashi da waya. Duk basirarsa ta kare, ya rasa na yi. Sai ya kara tunani yace “abunda zanyi shine in zauna a nan in jira, har sai turawan nan sun dawo. Na tabbata dole su fahimci cewa sun mance kudade da yawa. Amma nawa ne?”
A hankali sai ya saka hannu, ya debo damin daloli, yana waige-waige, ya ga babu wanda yake kallonshi, sai ya fara kirge. Bayan ‘yan mintuna ya gama. “Dala dubu biyu da dari uku” yace. Sai ya mayar da su, ya koma jikin bishiya ya jingina, gashi rana ta fara faduwa. Jim kadan, sai ya mike, ya duba nan, ya duba can ko zai hango katuwar bakar motar turawan da suka ajje shi, amma ina shiru kuke ji. Ba su dawo ba. Har ta kai ta kawo ya fara addu’a ko zasu dawo. Yana tsoron cewa motsi daya zai iya yi, motocin Hukumar FBI suyi masa taron dangi, su lalata masa shiri.

Can dare ya nitsa, gashi ‘yar gusau ta fara damunsa. Sai ya bude jakarshi, ya saka hannu a cikin wani tsohon takalminsa inda ya boye panke a cikin leda, ya dauko ya kai cizo. Annuri kuwa ta cika fuskarsa. Dama baturiya ta bashi robar ruwa irin na “swan water” a cikin mota kuma bai shanye ba. Sai ya bude ya kwankwada yayi gyatsa.

Kamar wasa, motoci suka rage zirga-zirga, amma garin fayau kamar rana saboda fitilu masu yawa dake haska kusan ko ina. A nan wajen yayi alwala, ya tayar da Sallah yayi kasaru. Yana cikin lazumi, can sai ya hango motar ‘yan sanda. Cikinshi ya tsure. A ranshi yace “shikennan, turawa sun mani cune.” Mota kuwa ko kula shi bata yi ba, ta wuce abunta. Gogan naku ya kwanta kamar wani maciji wai shi ya boye. A haka har bacci ya kwashe shi. Turawa kuwa babu su, babu alamarsu.

Can yana cikin bacci, sai yaji wani abu na tafiya a kusa da shi. Zuciyarshi ta buga, a ranshi yace “shikennan macijin Amurka ya harbe ni ya gama.” Bude idanunsa keda wuya, sai ga Kurege. Yana motsawa sai Kurege ya zura da gudu ya haye bishi kamar kadangare. Dan Kasa ya bi shi da kallo yana mamaki. Ya ji labaran kurege, amma yau gashi a gabansa. Duk tunanin nan da yake yi, ya manta yana sha’awar kama ruwa. Yana tunawa kuwa, sai yaji ya takura. Dubawa yake ya gani ko akwai inda zai iya zuwa, amma ina. A kusa da dogon ginin nan akwai wani shago da yayi kokarin karanta sunanshi dazu amma ya kasa. A ranshi yace “Su McDanals har yanzu ba’a bude ba”. Sai ya duba gefen dogon ginin, akwai wani lungu, yace “a can zan je in yi kaya na. Ba zan bari wannan abun ya kashe ni ba.” Jikinsa na dar-dar, ya rungumi GHANA-MUST-GO da sabuwar jakarsa ya nufi loko. Yana waige-waige kamar mara gaskiya, ya shige ya fara abunsa. Ai kuwa kamar wanda aka yiwa baki, shigarsa keda wuya, wata katuwar bakar mota tayi burki a bakin lokon. Wasu manya fararen fata suka fito daga ciki fuskokinsu babu annuri. Suna wani irin turanci kamar “harshen aljanu” suna matsawa kusa da shi a hankali. Shi kuwa yana ja da baya a hankali kuma gashi lokon baya bullewa. Sai ya fara cewa “sorry my friend bature, I am bery sorry walLahi”. Ko sauraronsa basu yi ba. Suka daga hannayensu suka kai masa naushi a fuska. Nan take ya fadi a sume.

Domin sauraron sautin wannan labarin, a latsa https://radiyontalaka.com/2020/06/02/labarin-dan-kasa-a-turai-2/

A biyo mu a kashi na gaba domin jin cigaban wannan labarin.

Dakta Bello Galadanchi

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.