Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya da ke fafutukar fadakarwa da kwato yancin mutanen arewacin tarayyar Najeriya Dokta Nasdura Ashir Sherif, ya bayyana cewa tun asali ma’aikatan Gwamnatin Najeriya ne suka koyawa yan siyasa yadda ake satar dukiyar yan kasa domin son ciziya kawai.
“A Najeriya kirkiro talauci aka yi domin wadansu masu son zuciya su samu biyan bukatun kansu, musamman idan aka yi amfani da yan kudi kalilan za a iya tankwara mutane su yi abin da ake bukata”.
Nasdura Ashir Sherif ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta Talbijin na Tambarin Hausa
Nasdura Ashir ya ci gaba da cewa tsarin da ake ciki a Najeriya na halin kakanikayi na gaf da kasancewa cikin yanayin da za a samu sauyin da ba a yi tsammani ba.
Sakamakon hakan ya sa muke kokarin fadakar da jama’a irin abin da ya dace musamman na hadin kai tsakanin Juna domin kasar ta samu ci gaba,”saboda mulki a hannun wadanda ake mulka yake ba hannun shugabannin ba, sai dai mun gano cewa an raba kawunan jama’a ne domin wata biyan bukata”.
“Muna fadakar da jama’a su Sani cewa duk wanda ya baka kudi cewa ka zabi wane ko wadansu mutane to, mama’s su Sani cewa ba makiyinka kamarsa, saboda me ya sa sai ya saye ka sannan zaka yi zabe kuma sai abin da yake so zaka zaba”.