Home / Labarai / MAGANAR ZA A KASHE NERA 500 DA 1,000 BA GASKIYA BANE – CBN

MAGANAR ZA A KASHE NERA 500 DA 1,000 BA GASKIYA BANE – CBN

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Gwamnan babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya bayyana cewa babu gaskiya a game da abin da wadansu kafofin yada labarai ke yadawa cewa wai a ci gaba da kashe takardun kudi na naira dari biyar (500) da naira dubu daya (1,000), sam ba gaskiya bane.
A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Daraktan da ke kula da bangaren harkokin yada labarai na babban Bankin Najeriya Mista Osita Nwanisobi ya sanyawa hannu na cewa kudin da kawai aka amince da a ci gaba da kashewa tsawon watanni biyu wato kwanaki Sittin masu zuwa har ranar 10 ga watan Afrilu, 2023, sune naira dari biyu kawai babu maganar naira dari biyar 500 ko dubu daya 1,000  a ciki .
Osita ya ci gaba da cewa game da batun naira dari 500 da dubu daya 1,000 sai dai kowa mutum da yake da su ya ta fi Bankin da yake hulda da shi ya kai tsohon kudin naira dari 500 da 1,000 idan ya na da su har naira dubu dari biyar (500,000) za a gaya masa bayanan da  ake nema idan za a ajiye kudin a Bankin nasa.

About andiya

Check Also

Dangote cement export of clinker, cement increase by 87.2%

  Management of Dangote Cement Plc has revealed that the company dispatched seven ships of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.