Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga majalisar dokokin Jihar Kaduna na cewa daukacin majalisar duk sun bayyana dawowa daga Rakiyar jagorancin Moh Haruna Inuwa da ake wa lakabi da ( Mabo) shugaban masu rinjaye na majalisar.
Bayanin hakan ya fito ne lokacin da majalisar za ta yi wani zama, inda kafin majalisar ta zauna aka bayar da mihimmiyar sanarwa a kan hakan.
” Kafin mu fara aiwatar da komai a zaman majalisar na yau, akwai sanarwa ta musamman shi ne majalisa ta dawo daga Rakiyar shugabancin shugaban masu rinjaye Haruna Inuwa, kuma za a bayyana shugaban masu rinjayen a nan gaba”, inji sanarwar majalisar.
Mataimakin shugaban majalisar dokokin Jihar kaduna ,honarabul Isaac Auta Zankai ne ya bayar da sanarwar kafin zaman majalisar.