Home / Labarai / MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KATSINA TA DAKATAR DA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR FASKARI

MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KATSINA TA DAKATAR DA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR FASKARI

 

Sakamakon irin yadda wadansu mutane yan asalin karamar hukumar Faskari suka Gabatarwa da majalisar dokokin Jihar Katsina karkashin jagorancin Honarabul Tasi’u Maigari Zango korafi majalisar ta Dakatar da shugaban karamar hukumar ta Faskari Bala Ado har sai sun kammala gudanar da binciken da suke yi a kansa.

 

Majalisar dokokin da ke karkashin Honarabul Tasi’u Maigari Zango ta ce sun dauki wannan matakin ne har sai ta kammala gudanar da binciken da take yi a kan shugaban karamar hukumar Honarabul Musa Ado, domin dakatarwar za ta bayar da damar a gudanar da binciken kamar yadda doka ta tanadar.

 

Kamar yadda muka shaida maku a tun farko majalisar ta dauki wannan matakin ne sakamakon irin korafin da wasu yan asalin karamar hukumar su biyar suka gabatar a gabanta a ka shugaban karamar hukumar.

Wadanda suka gabatar da korafin sun hada da; Ashiru Danjuma (Ashow), Sulaiman Muhammad, Hamisu Haruna, Halilu Umar da kuma Shamsu S.Hussaini, inda suka bayyana cews suna zargin Shugaban karamar hukumar ta su ne, da sabawa dokokin mulki inda a cikin korafin nasu suka bayyana cewa.

“Shugaban karamar hukumar na kashe sama da dubu ɗari biyu da hamsin N250,000 daga cikin asusun gwamnati, duk wata, wanda hakan ya saba wa doka ta 88 (2) (a) da ke cikin kundin kananan hukumomi mai lamba.4 da aka yi wa gyara a shekarar 2023, inda dokar ta ambaci kashe sama da waɗanda kudade sai da amincewar Majalisar Kansiloli ta karamar hukuma”.

Haka kuma masu zargin sun bayyana cewa “shugaban karamar hukumar ya saba wa doka ta 41 (2) cikin baka da ke cikin kundin dokokin kananan hukumomi na 2023 doka mai lamba No.4 wadda ta ayyana cewa tilas idan shugaban karamar hukuma zai nada Kansiloli masu ofis sai ya turo wa Majalissar Kansiloli sun tantance su.

Sun kuma yi korafin cewa gwamnatin jihar Katsina ta turo makudan kudade na wata-wata  da shugaban karamar hukumar ya karba kuma baya iya bayyana abin da ya yi da kuɗaɗen ko hanyar da ya bi wajen kashe kudaden bisa doka, kamar yadda za ku gani a cikin takardun koken da ke a gabanku ya ku yan majalisa.

Bayan karanta korafin, duk yan majalisar da suka halarci zaman sun aminta da a yi bincike game da korafin tare da dakatar da shugaban karamar hukumar har sai kwamitin majalisar ya kammala bincikensa game da korafe-korafen da aka kawo masu a zauren majalisar.

Ga dai wadanda suka gabatar da korafi a kan shugaban karamar hukumar Faskari da suka gabatar a gaban majalisar dokokin Jihar Katsina

 

Tuni dai majalisar dokokin ta mika batun ga kwamitin majalisar mai kula da sauraren korafe – korafen da jama’a suka Gabatarwa majalisar domin ci gaba da aikin bincike a kan lamarin

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.