Home / Labarai / Likitoci Masu Neman Kwareww Sun Shiga Yajin Aiki A Najeriya

Likitoci Masu Neman Kwareww Sun Shiga Yajin Aiki A Najeriya

Sakamakon irin yadda aka samu kudewar al’amuran kula da walwalar Likitoci musamman masu neman kwarewa a tarayyar Najeriya ya sa kungiyar tasu ta bayar da sanarwar tafiya yajin aikin gargadi na kwanaki Biyar daga yau Laraba zuwa ranar litinin 22 ga wannan watan.
Kamar dai yadda bayanai suka gabata Likitocin masu yajin aikin sun ce a cikin bukatun da suke nema a biya masu akwai kudin alawus – alawus, inganta walwalarsu rare da inganta albashinsu Baki daya.
Da wakilinmu ya zagaya wasu daga cikin asibitocin ya ganewa idanunsa kamar haka ya ga marasa lafiya sun cika makil kasancewar wurin ne ake duba marasa lafiya amma saboda yajin aikin da Likitocin suka shiga marasa lafiyar na cikin wani mawuyacin hali.
Kasancewar fuskokinsu da dama daga cikinsu na cike da damuwa, abin da ke nuna cewa yajin aikin na kwanaki biyar ya fara tasiri.
“Wani mara lafiya ya shaida masa cewa ya zo ne daga jihar Gombe, kasancewarsa yazo ne daga wuri mai nisa da nufin a duba dan uwansa, amma tun safe ba su kai ga ganin likita ba. Likitocin masu neman kwarewa sun shiga yajin aikin saboda a cewarsu gwamnati ta gaza biya musu bukatunsu ciki har da inganta albashi”.
Dakta Abubakar Nagoma Usman, shugaban kungiyar likitocin na arewa maso yamma, ya ce bayan kwana biyar za su koma bakin aiki, sannan su kira taron kungiyar na ƙasa, inda za a bibiyi inda aka kwana tare da ɗaukar mataki na gaba idan gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba.
Marasa lafiya da waɗanda suke kula da su tuni suka fara ficewa daga asibitin don zuwa wani wurin da walau su biya kuɗi a duba su ko kuma asibitin gwamnatin jiha.
Ba wannan ne karon farko ba da likitoci masu neman kwarewa ke shiga yajin aiki, ko a 2021 ma, sau huɗu cikin shekara guda likitocin na yajin aiki, a wani mataki na matsawa mahukunta lamba don su biya musu bukatunsu.
Wannan batu na yajin aikin dai akasari marasa lafiya ne ke shiga tasku kasancewar babu isassun likitoci da za su duba su.
Lamarin yajin aiki dai a Najeriya na cikin wani mawuyacin hali kasancewa ba kawai Likitoci ke fama da matsalolin da suke haifar da yajin aikin ba har ma da sauran dukkan bangarorin ma’aikata suke masu zaman kansu da dai sauransu.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.