Home / Labarai / Majalisar Dokokin Jihar Katsina Ta Tabbatar Da Kagara A Matsayin Kwamishina

Majalisar Dokokin Jihar Katsina Ta Tabbatar Da Kagara A Matsayin Kwamishina

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

A ranar Laraba ne Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta kammala tantance sunayen kwamishinonin da Gwamnan Jihar Malam Dikko Umar Radda ya mika mata.

An kammala aikin tantancewar tare da wanke dukkan wadanda aka nada tare da tabbatar da su a matsayin mambobin majalisar zartarwa ta jiha.

Alhaji Bello Husaini Kagara na daga cikin wadanda aka tantance,tare da tabbatar da su a matsayin Kwamishina kuma dan majalisar zartarwa ta Jihar.

Majalisar Dokokin Jihar ta bayyana Bello Kagara a matsayin daya daga cikin fitaccen masanin ilimi, gogaggen dan siyasa wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen bunkasa ilimi da kuma nasarorin da jam’iyyar APC ta samu a zaben da ya gabata.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan an tantance shi, Alhaji Bello Kagara ya jaddada kudirinsa na taimakawa gwamnatin Radda domin samun nasara a dukkan ayyukanta.

Bello Kagara ya mika godiyarsa ga majalisar bisa karbewar da aka yi masa da kuma yadda jama’a suka yi ta murna a lokacin da aka kammala tantancewar.

Ya bayyana fatan sauran mambobin majalisar zartaswar jihar za su yi aiki tukuru domin samun nasarorin da ake bukata ta yadda za a samu ci gaban jiha da kasa baki daya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.