Home / Labarai / GWAMNA LAWAL YA KARRAMA HAJIYAR DA TA MAYAR DA DALA 80,000 A SAUDIYYA

GWAMNA LAWAL YA KARRAMA HAJIYAR DA TA MAYAR DA DALA 80,000 A SAUDIYYA

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Alhamis, ya karrama alhazan da ya mayar wa mai shi dala 80,000 a lokacin aikin Hajjin da ya gabata a kasar Saudiyya.

Mahajjaciyar, Hajiya Aishatu ‘yan Guru Nahuce daga karamar hukumar Bungudu a Jihar Zamfara ta samu dala 80,000 (N64,240,000) sannan ta mika ta ga jami’in hukumar jin dadin alhazai ta Zamfara domin mayarwa mai kudin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce Gwamnan ya karrama maniyyaciyar ne tare da dukkan sarakunan jihar, wanda ya gudana a zauren majalisar da ke gidan gwamnati.

Gwamnan ya kuma bayyana matukar farin cikin da gwamnatin jihar ta nuna kan sahihancin alhazan.

“Dukkan al’ummar Jihar Zamfara suna alfahari da farin ciki kan abin da Hajiya A’ishatu ta yi a Saudiyya, ya kara wa daukacin al’ummar Kwarjini da kyakkyawan suna a fadin duniya baki daya.

“Abin alfahari ba ne a gare mu  Hajiya A’isha ba, ta rubuta sunanta a cikin litattafan tarihi masu kyau, irin wannan abin ana so ne ga duk wani Musulmi mai aminci, musamman a kasa mai tsarki ya tabbatar da nuna hali mai kyau”.

“Mun ga misali karara na gaskiya da ya kamata a yi koyi da Hajiya A’isha, domin ba kowa ne zai iya samun irin wadannan makudan kudade a wurin da ba kowa, ya mayar da su ba.

“Gwamnatin Jihar Zamfara za ta yi abin da ya dacesomin duk mai bukatar taimakawa iyalan Hajiya Aisha.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuma zai karrama Hajiya A’isha bisa wannan aiki na gaskiya.”

Tun da farko, Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru yayin gabatar da Hajiya A’isha, ya jaddada cewa matakin da ta dauka ya kara mutunta al’ummar Zamfara baki daya.

Hajiya Aisha ta kuma bayyana yadda lamarin ya faru a kasa mai tsarki a kasar Saudiyya.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.