Home / Ilimi / Makarantar Cherry Hearts Ce Za Ta Taimakawa Najeriya Da Afirka Baki Daya – Rabi’u Musa

Makarantar Cherry Hearts Ce Za Ta Taimakawa Najeriya Da Afirka Baki Daya – Rabi’u Musa

Mustapha Imrana Abdullahi
Honarabul Alhaji Muhammad Rabi’u Musa, shugaban Gidauniyar Almuharram da ke aikin kula da taimakon mabukata musamman marayu da marasa galihu ya bayyana makarantar Cherry hearts  da cewa wuri ne da ake kokarin gina al’umma da nufin samun manyan gobe da za su yi wa kasa ayyukan ci gaba.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wakilinmu lokacin da ya halarci babban taron saukar karatun daliban da suka sauke Alkur’ani karo na biyu da aka yi a harabar makarantar da ke kan titin Isa Kaita cikin garin Kaduna.
“Ina da yara guda biyu a cikin wadanda suka sauke Alkur’ani don haka ne muka taru a wannan makaranta domin yin murna da kyautar ilimin Alkur’ani da Allah madaukakin Satki ya yi wa yaran kyauta da shi, muna murna kwarai da farin ciki”.
Alhaji Rabi’u Musa ya ci gaba da cewa hakika wannan makaranta ta Cherry hearts Academy da ta kasance a kalla tsawon shekaru uku da suka gabata su na da ingantattun tsare tsaren Koyar da ilimin addini da na Boko da kowane mahaifi zai so dansa ya kasance ya na karatu a wannan makaranta saboda ingancin da take da shi, saboda ni a matsayi na hakika na gamsu da irin yadda suke tafiyar da harkokin iliminsu”.
Rabi’u Musa ya kuma yi kira ga iyayen yara tare da fadakar da su cewa ya dace kowa ya Sani cewa ba za a iya hada nagartar ilimi da duk wani batu na  kudi ba a duniya, don haka iyaye kawai su dage wajen kokarin biyawa yayansu kudin makaranta domin samun ilimi mai inganci, inda ya bayar da misali da kansa da ya ce shi a matsayinsa na dan kasuwa ba shi da lokacin da zai tsaya har ya karantar da yayansa sai dai kawai ya rika addu’ar Allah ya bashi yadda zai biya wa yara kudin makaranta don haka babu abin da mutum zai hada da ilimi domin da shi ne ake samun biyan bukata har su yaya su zama wani abu a rayuwarsu.
“Hakika na lura da wani abu a wannan makaranta wato jinjinar Alasan barka ga shugabannin gudanarwar wannan makaranta, don haka muke kara yin kira a gare su da su kara himma wajen inganta al’amuran wannan makaranta ta Cherry heart Academy da nufin kwalliya ta biya kudin sabulu”.
Ya kara da cewa hakika wannan makaranta ta cancanci kowane mahaifi ya dauko yayansa ya kawo wannan makaranta domin muna ganin muhimmancinta kwarai
Muhammad Rabi’u Musa ya bayyana gidauniyar Almuharram da cewa ta na gudanar da ayyukan taimakawa marayu da marasa galihu ne a cikin al’umma, ta hanyar daukar nauyin karatunsu da kuma biya masu kudi su rubuta jarabawar shiga manyan makarantun gaba da Sakandare (JAMB) domin rayuwarsu ta inganta kamar kowa.
“Ko a wannan satin da ya gabata mun dauki nauyin wadansu yara guda biyar da a yanzu an kammala komai sai kama karatu kawai a cikin sati mai kama wa

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.