Gwamnonin jihohin Katsina, Aminu Bello Masari da na Kano Abdullahi Ganduje sun ziyarce Gwamnan jahar Sokoto da maraicen yau a Sokoto don gabatar da sakonni gwamnati da al’ummar jihohin su dangane da kisan gilla da aka yiwa wasu matafiya a garin Sabon Birni da sauran haren haren ta’addanci da suka faru a lokuta dabam dabam a jihar Sokoto.
Gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ne ya karbi bakuncin su tare da sauran mukkaraban gwamnatin jaha.
Allah Ya saka da alheri ya kawo saukin wadanan matsalolin, ameen.
Dingyadi Media