Masari Ya Kaddamar Da Motocin Kashe Gobara Guda Biyu
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya kaddamar da Motocin Ƙashe gobara guda 2 ɗaya Shiyyar Daura, ɗaya kuma a makarantar kashe gobara ta Arewa masu Yamma da ke ƙaramar hukumar Kankiya wadda Sanator Ahmad Babba Kaita ya nemo a zauren majalisar Dattawa ta kasa.
An kaddamar da wadannan motoci ne a fadar Gwamnatin jihar katsina ƙarkashin Shugaban hukumar Kashe Gobara ta ƙasa Alhaji Ibrahim Liman Alhaji, ya kawo wannan motoci domin damƙama Gwamnatin jihar katsina su kafin kai kowace mazauninta da za a ci gaba da aiki da su.
A cikin Jawabin Maigirma Gwamna Masari a lokacin da yake ƙaddamar da motocin ya yabama Sanator Ahmad Babba Kaita daya jajirce wajen kawo irin wannan ci gaba a jihar katsina, tare da hukumar kashe gobarar ta kasa da irin wannan kokari da suka yi domin ganin kafuwar wannan makaranta tare da zuwan wannan motoci jihar katsina.